Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

[ad_1]

Wakilai daga jihohin Kebbi, Ekiti, Bauchi da wasu jihohi da dama sun jagoranci harkokin taron kasa na shekarar 2026 na jam’iyyar PDP, wanda Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya mara wa baya.

Jam’iyyar ta bayyana sabbin mambobi 19 na Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) a dakin taro na filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, a wani mataki na sake farfado da babar jam’iyyar adawa.

  • Kasar Sin Ta Hau Matsayi Na 9 A Ma’aunin Kirkire-Kirkire A Duniya
  • Ƴan PDP Sun Fara Taruwa A Abuja Don Halartar Babban Taron Jam’iyyar Na Ƙasa

Mun rahoto tun a baya cewa, tsagin PDP mai goyon bayan Wike ta amince da shirin zaben mambobin NWC, wadanda za su kula da harkokin jam’iyyar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Ga jerin Mambobin NWC, da aka amince da su, kamar haka:

Shugaba – Abdulrahman Mohammed; Mataimakin Shugaba (Kudu) – Aaron Chukwuemeka; Mataimakin Shugaba (Arewa) – Yusufu Akirikwen (SAN); Sakatare – Anyanwu Samuel; Mataimakin Sakatare – Kolawale Olabisi; Ma’aji – Odeyemei Oladiran; Mataimakin Ma’aji – Lado Marke.

Sauran mukaman sun hada da: Sakataren Kudi – Eyim Henry; Mataimakin Sakataren Kudi – Dr Grema Kyari; Sakataren Tsare-tsare – Umar Bature; Mataimakin Sakataren Tsare-tsare – Efere Augustine.

Har ila yau, akwai: Sakataren Yada Labarai – Jungudo Mohammed; Mataimakinsa – Egwu Chidiebere; Lauyan Jam’iyya – Kamaldeen Ajibade (SAN); Mataimakin Lauya – Aloysius Uba; Mai binciken kudi – Osuoha Donatus; Mataimakinsa – Dr Adaba Yatu; Shugaban Matasa – Ibrahim Aboki; Mataimakinsa – Momoh Bashir.

Farfesa Ogunshe Adedayo, itace ke rike da mukamin Shugabar Mata, yayin da Hauwa Shinge ta zama Mataimakiyarta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *