Ni da Netanyahu ne za mu yanke shawarar kawo ƙarshen yaƙin Iran — Trump

[ad_1]



Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ne za su yanke shawara kan batun kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran.

Jaridar The Times of Israel ta ruwaito cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta waya, inda ya ce shi da Netanyahu sun shafe lokaci suna tattaunawa kan batun.

“Ina ganin shawarar za ta kasance ta haɗin gwiwa ne… mun dade muna magana kan batun. Zan yanke hukunci a lokacin da ya dace, amma za a yi la’akari da komai,” in ji Trump lokacin da aka tambaye shi ko shi kaɗai ne zai yanke hukuncin kawo ƙarshen yaƙin.

Da aka tambaye shi ko Isra’ila za ta iya ci gaba da yaƙi da Iran idan Amurka ta dakatar da hare-haren da take kai wa, Trump ya ce bai ga hakan zai zama dole ba.

Dangane da yadda farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo a kasuwar duniya a dalilin yaƙin, Trump ya ce tashin farashin na wani ɗan lokaci ne, kuma gara ɗaukar wannan ƙaddarar a kan barin Iran ta mallaki makamin Nukiliya


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *