Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram – UNICEF
[ad_1]
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya kiyasta cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 10, kwatankwacin Naira tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana hakan a Maiduguri ranar Laraba yayin ƙaddamar da wani shirin farfaɗo da rayuwar yara da rikici ya shafa ta hanyar ba su horo da tallafi.
An wakilta Saeed ta hannun Manajan Kare Yara na UNICEF, Shah Mohammad Khan, inda ta ce rikicin da ya daɗe ya rage girman tattalin arzikin ƙasar, ya kuma lalata samun kuɗin shigar iyalai da matasa a yankin.
Ta ce, “A cewar wani bincike da UNICEF ta gudanar a shekarar 2024, asarar tattalin arzikin da rikici ya haifar a Arewa maso Gabas ya kai dala biliyan 10 cikin shekaru goma da suka gabata.
“Rikici ba wai kawai ya raunana tattalin arzikin ƙasa ba ne, har ma ya durƙusar da samun kuɗin shiga da damar aiki ga iyalai da matasa.
“Tsawon lokaci, yara da matasa da dama, musamman ’yan mata, ba su samu damar koyon sana’o’i ko cika burinsu ba,” in ji ta.
Wakiliyar ta UNICEF ta kuma nuna damuwa kan yadda shekaru da dama na rikici a yankin suka kasance da munanan laifuka kan yara, ciki har da sace-sace da cin zarafi ta hanyar jima’i, tare da cewa rasa damar samun abin dogaro da kai ya shafi ci gaban ɗan adam sosai.
A cewarta, sabon shirin farfaɗo da rayuwa da aka ƙaddamar yana da nufin tallafa wa yaran da rikicin ya shafa ta hanyar koyar da su sana’o’i da kuma ba su kariya ta musamman.
“Yanzu haka, yara 1,033, maza 567 da mata 466, na amfana da horon sana’o’i a cibiyoyi daban-daban a Maiduguri, Bama, Biu, Damboa da Konduga,” in ji ta.
Saeed ta bayyana cewa ana koyar da yaran sana’o’in da za su iya amfani da su a rayuwa kamar dinki, fasahar sadarwa, gyaran motoci, ƙera takalma da sana’ar kafinta.
Wafa Saeed ta kuma ce fiye da yara 1,000 ana sa ran za su amfana da shirin a kowace shekara, inda za su samu ƙwarewar da za ta buɗe musu ƙofofin aiki da rayuwa mai ɗorewa.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Borno, Abba Wakilbe, ya yaba wa UNICEF da sauran abokan hulɗarta irin su UNDP, IOM da UNODC, kan goyon bayan da suka bayar a shirin.
“Ina so in gode wa UNICEF musamman bisa taimakon da ta ba mu a lokutan da muka shiga mawuyacin hali,” in ji Wakilbe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link