Na Yi Murabus Ne Saboda Dalilai Na Ƙashin Kaina – Shugaban Hukumar Aikin Hajji

[ad_1]

Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman, ya tabbatar da murabus ɗinsa a hukumance.

Farfesa Usman, ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.

  • GDP A Nijeriya Ya Taba Zarce Na China Da Malaysia Lokacin Da Muka Yi Watsi Da IMF — Gbenga Hashim
  • Shekaru 55 Da Kulla Diflomasiyya: Akwai Kyakkawar Huldar Abota Tsakanin Sin Da Najeriya

Tsohon shugaban hukumar NAHCON, a cikin sanarwar, ya musanta zargin aikata wani laifi, yana mai jaddada cewa, ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa ne kawai saboda dalilai na ƙashin kansa.

Ajiye aikin nasa ya biyo bayan rahotannin da ke cewa, hukumar NAHCON ta gabatar da takardar koke ga Shugaba Bola Tinubu inda ta yi kira da a cire shi saboda zargin rashin ɗa’a.

Takardar, mai kwanan wata, 19 ga Janairu, 2026 kuma mambobin kula da hukumar 11 suka sanya wa hannu, an yi mata taken “Ƙuri’ar Rashin Amincewa da Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa ta Nijeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman”.

Takardar na zargin tsohon shugaban hukumar da rashin da’a, rashin gaskiya, da kuma amincewa da kashe kuɗi akai-akai da kuma bayar da kwangiloli ba tare da amincewar mambobin kula da hukumar ba, fiye da kasafin kuɗin hukumar.

A cewar takardar, “ayyukan shugaban sun zama masu keta dokokin kuɗi, wanda kuma a halin yanzu, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) tana bincikensa”.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *