Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe

[ad_1]



Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe.

Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta.

Mutumin da ake zargi da wannan aika-aikar mai suna Rabilu Sani, ɗan kimanin shekara 22, an gano cewa yana ɗauke da cutar kanjamau (HIV), kamar yadda mahaifin yarinyar ya tabbatar wa manema labarai.

A wata hira da aka yi da mahaifin ta ta wayar tarho, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin Jakusko tare da wanda ake zargi, inda likita ya gudanar da gwaje-gwaje, kuma sakamakon ya tabbatar da cewa mutumin na ɗauke da cutar HIV.

A halin yanzu, wanda ake zargi yana hannun jami’an ’yan sanda na Jakusko, inda ake ci gaba da gudanar da bincike, kamar yadda baturen ’yan sandan yankin ya bayyana wa manema labarai.

Ya ƙara da cewa da zarar an kammala bincike, za a miƙa wanda ake zargin ofishin su da ke Damaturu, fadar jihar, domin zurfafa bincike, kafin daga bisani a samu ƙarin bayani daga bakin kakakin rundunar a matakin jiha.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *