Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba.

Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba.

A cewarsa, jam’iyyar PDP “ta mutu tun tuni,” kuma ba ya cikin waɗanda za su nemi farfaɗo da ita.

Ya ƙara da cewa yawancin gwamnonin da suka rage a PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

“Ba daidai ba ne a zargi Tinubu saboda ficewar Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, zuwa APC,” in ji Fayose.

“Su da kansu suka yanke shawara saboda PDP ta rasa shugabanci da tsari.”

Fayose, wanda ya mulki Ekiti sau biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya ce jam’iyyar ta kasa koyon darasi daga kurakurenta na baya, kuma ya sa ta zama mai rauni.

Ya kuma zargi wasu shugabannin PDP da yin siyasa don amfanin kansu maimakon ci gaban jam’iyyar gaba ɗaya.

Maganganunsa na zuwa nedaidai lokacin da ake cece-ku-ce a Najeriya kan yiwuwar komawa tsarin jam’iyya ɗaya, yayin da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa ke ci gaba da komawa APC gabanin zaɓen 2027.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *