Idan Gwamna Abba Ya Ziyarci Kwalejin Bebeji Matsalarmu Za Ta Zo Ƙarshe – HOD Habib
[ad_1]
Shugaban sashin kula da koyar da ilimin kiwon lafiya na kwalejin kimiya da fasaha ta lafiya ta Bebeji, Malam Auwal Shehu Habib ƙarƙashin shugabancin Malam Sulaiman Abdullahi ya bayyana cewa idan Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ziyarci kwalejin ya ga nasarori da matsalolin da kwalejin ke fuskanta, matsalolin za su warware kuma nasara za ta ƙaru a wannan makaranta.
Malam Auwal ya bayyana haka ne a wajen rantsar da ɗaliban makarantar da suka kammala karatu a fannin kula da lafiyar al’umma tun daga tushe wanda hukumar kula da waɗannan makaranta ta tabbatar da ingancinsu da rantsar da su a matsayin ma’aikatan kiwon lafiya da suka samu horo.
An dai gudanar da taron ne a ranar Juma’a da ta gabata a jami’ar ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Kano.
- Daga Ranar 1 Ga Maris, Za A Fara Hutun Zango Na Biyu Na Makarantu A Kano
- Za A Fara Hukunta Matan Da Ke Zama A Gefen Direban Adaidaita A Kano
HOD Auwalu ya ce gwamnatin Kano ta yi ƙoƙari wajen samar da tsarin fasahar sadarwa a kwalejin ta Bebeji da sauran abubuwa wanda kwalejin ke alfahari da su daga wannan gwamnati ta Abba.
A cewarsa, wannan makarantar na samun ci gaba sosai tun zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar, Sanata Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a shekarar 2012.
Haka kuma ya ƙara da cewa matsalar da makaranta take fuskanta sun haɗa da ƙaranci ajujuwa, wanda makarantar na da tarin ɗalibai, ga matsalar gurin kwanan ɗalibai, sannan kuma gwamnatin Abba ta sanar da cewa ta bai wa makaranta mota amma har yanɗu motar ba ta zo ba, haka kuma an yi alƙawari gyaran tsarin makarantar, an kuma bayar a gwamnatance abin bai zo ba, saboda haka zuwan Gwamna Abba zai sa ya ga matsaloli da nasarori da ɗaukar mataki cikin sauri wajen ci gaban Kano.
A ƙarshe, HOD Auwalu ya bayyana ɗaliban makarantar masu ƙwazo ta yadda ba a samu ƙasa da kashi 90 cikin 100 har zuwa 100 bisa 100 wanda suka gama makarantar cikin nasara da samu horo na yadda za su nuna kyakywar mu’amala da tausayawa masu jinya da masu larura bisa koyarwar adinin da aladu masu kyau. Ya yaba wa hukumomi irinsu asusun kula da manyan makarantu ta ƙasa (Tetfund) da sauran masu ruwa da tsaki wajen ci gaban wannan kwaleji ta Bebeji da ke Kano.
[ad_2]
Source link