HOTUNA: Yadda Iraniyawa ke murnar naɗin sabon jagora Mojtaba Khamenei

[ad_1]



Dubban mutane sun yi dandazo a birnin Tehran domin yi wa sabon jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei mubaya’a, bayan sanar da naɗinsa a matsayin jagoran ƙasar.

Rahotanni sun ce jama’ar sun fito kan manyan tituna da filayen taro a birnin, suna ɗaga tutocin Iran da kuma hotunan sabon jagoran, yayin da wasu ke rera taken goyon baya.

Wannan dai na zuwa ne bayan Majalisar Masana ta Iran ta zaɓi Mojtaba Khamenei a matsayin jagora na uku tun bayan juyin juya halin Musulunci na 1979, domin maye gurbin mahaifinsa, Ali Khamenei da aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.

Magoya bayan gwamnatin Iran suna murnar naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar.

Hotunan da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya wallafa sun nuna dubban mutane suna taruwa a wurare kamar Dandanlin Vali-Asr, inda suka riƙa taya juna murna tare da nuna goyon baya ga sabon jagoran ƙasar.

Iraniyawan sun buƙaci sabon jagoran ya kawo ƙarshen kwanaki na rashin tabbas da ƙasar ta shiga bayan mutuwar tsohon jagoran.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *