Harin Bam A Maiduguri: Har Yanzu Akwai ’Yan Ƙunar Baƙin Wake Biyu Da Suka Yi Ɓatan Dabo – Zulum
[ad_1]
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya tabbatar da cewa har yanzu ana neman ragowar ‘yan kunar bakin wake biyu da suka yi ɓatan dabo a cikin Maiduguri bayan hare-haren fashewar bama-bamai da suka faru a babban birnin jihar.
Da yake magana a wata hira da BBC Pidgin, Zulum ya ce rahotannin sirri sun nuna cewa ’yan kunar bakin wake guda biyar ne suka kutso cikin birnin, inda uku daga cikinsu tuni suka tayar da bama-bamansu, yayin da har yanzu ba a san inda sauran biyun suke ba.
- Burina Na Gaba Bayan Fim Shi Ne Aure —Khadija
- Warware Batun Taiwan Lamari Ne Da Ya Shafi Kasar Sin Ita Kadai
“Kamar yadda na fada a baya, bayanan sirri da muka samu zuwa yanzu sun nuna cewa ’yan kunar bakin wake guda biyar ne suka shigo Maiduguri. Zuwa yanzu, uku daga cikinsu sun tayar da bama-bamansu, yayin da ake ci gaba da bincike kan inda sauran biyun suke,” in ji gwamnan.
Hare-haren da aka kai a lokaci guda, sun jikkata sama da mutum 100 tare da janyo mutuwar mutane 23. Hukumomi sun nuna damuwa kan sake kutsen ’yan ta’adda, musamman a lokutan bukukuwa kamar na Eid-el-Fitr.
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya bayyana cewa wasu daga cikin bama-baman an dauko su ne ta hanyar babura masu kafa uku (keke Napep) domin kauce wa binciken jami’an tsaro.
Zulum ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na ci gaba da bin sawun sauran ’yan kunar bakin waken tare da kara tsaurara matakan sa ido a fadin birnin. Ya kuma bukaci mazauna yankin da su cigaba da kasance cikin taka tsantsan tare da gujewa wuraren cunkoson jama’a.
[ad_2]
Source link