Dalilin da ya sa na tsere Kamaru bayan Boko Haram ta ƙone fadata a Borno — Basarake

[ad_1]



Dagacin garin Kirawa a Ƙaramar Hukumar Gwoza, a Jihar Borno, Abdulrahman Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsere daga Najeriya zuwa Kamaru bayan harin Boko Haram.

A farkon makon nan, mayaƙan Boko Haram sun kai hari garin Kirawa, inda suka kashe mutum biyu sannan suka ƙone fadarsa.

A hirar da aka yi da shi, Abubakar ya ce babu wani zaɓi da ya rage masa face ya tsere.

“Babu abin da ya rage sai na tsere zuwa Kamaru. Mazauna garin sun hau manyan motoci sun tsallaka iyaka, wasu kuma sun gudu zuwa Maiduguri.”

Boko Haram ta saki bidiyo da ke nuna yadda mayaƙanta suka ƙone barikin sojoji.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 5,000 ne suka tsere zuwa Kamaru saboda hare-hare a Gwoza.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya kai ziyara yankin da aka kai harin a ranar Juma’a.

Ya tunatar da dakarun Najeriya muhimmancin kare garuruwan da ke kan iyaka irin su Kirawa, Baga, Damasak da Malamfatori.

Zulum, ya ce sojojin Kamaru sun taimaka wajen dawo da jama’a garuruwansu shekarun da suka gabata, amma janyewarsu ya haifar da ƙalubalen tsaro.

“Abin takaici, gargaɗin da na yi bai samu karɓuwa ba. ’Yan ta’adda sun sake kai hari a ranar Laraba, sun kashe mutum biyu, sun kuma ƙone gidaje 50, motocinmu guda takwas da manyan injina. Mun gode wa Allah cewa ba a rasa rayuka masu yawa ba,” in ji gwamnan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *