Category: Latest News

  • Yadda zaɓen ƙananan hukumomi ke gudana a Jihar Ribas

    [ad_1]

    A yau Asabar ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Ribas.



    A yau Asabar ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Ribas.

    Hotuna: Bassey Willie


    [ad_2]

    Source link

  • A Karo Na 3 Cikin Wata Guda, Jirgin Ruwa Ya Sake Kifewa A Sakkwato

    [ad_1]

    Jihar Sokoto ta sake fuskantar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa, karo na uku a cikin wannan watan, inda aka tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da aka ceto mutane tara.

    Hatsarin ya faru ne da yammacin Juma’a a kogin Jaranja da ke ƙaramar hukumar Shagari, kamar yadda Shugaban Hukumar Ruwa ta Ƙasa (NIWA) a Sokoto, Bala Bello, ya tabbatar. Ya ce hatsarin ya samo asali ne daga sakaci, da ɗaukar kaya da fasinja fiye da ƙima da kuma karya ƙa’idojin tafiya a ruwa lafiya.

    Kungiyoyin ceto da ta suka haɗa da jami’an NIWA, da hukumar NEMA, da hukumar SEMA ta jiha, da kuma Red Cross sun shiga aikin ceto da bincike domin gano waɗanda ake zargin sun ɓace. Bello ya bayyana cewa suna ci gaba da wayar da kan al’ummomin da ke zaune a bakin ruwa kan muhimmancin amfani da rigar kariya/ceto ta ruwa da kuma bin ƙa’idojin zirga-zirga a ruwa.

    A ranar 17 ga Agusta, gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar fasinjoji huɗu tare da mutane 41 da aka ceto da kuma mutane biyar da suka ɓace a wani hatsarin jirgin ruwa a ƙauyen Kojiyo, ƙaramar hukumar Goronyo. Haka kuma, a ranar 22 ga Agusta, wani hatsari ya auku a ƙauyen Faji na ƙaramar hukumar Sabon Birni. Wannan ya sa hatsarin ranar Juma’a ya zama na uku a cikin wata guda.

    Shugaban Sashen Ceto da Farfaɗo da NEMA, Malam Tukur Abubakar, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin ceto domin gano fasinjan da ake nema. Wani mazaunin yankin, Malam Abubakar Jabbi daga La, ya ce masu linƙaya sun ceto mutane tara, sun kuma hango gawar mutum ɗaya, yayin da ake ci gaba da neman gawar wata mata da ta nutse.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • 2027: ’Yan Najeriya suna fama da yunwa, sun san abin da za su yi — Kwankwaso

    [ad_1]



    Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

    Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci. Wasu sun rasa matsugunansu saboda rashin tsaro. Wasu kuma suna asibiti ba tare da kulawa ta gari ba—ko kuma ba za su iya zuwa ba saboda babu kuɗi a hannunsu.

    “Mutanen wannan kasa sun yanke shawara kan abin da za su yi a 2027. Shi ya sa muke farin ciki da kanmu—saboda muna tare da jama’a. Kuma jama’a sun san muna tare da su. Ba mu gamsu da abubuwa da dama ba da suke faruwa a faɗin kasar nan, musamman batun talauci.

    “Talauci ya mamaye ƙasar nan, musamman a wannan yanki (arewa). Talauci ne mai tsanani. Al’ummomi da dama ba za su iya zuwa gona ba. Wasu ba za su iya zuwa kasuwa ba. Wasu ma ba za su iya komawa gidajensu ba.”

    Kwankwaso ya gargaɗi mambobin NNPP da kada su bari sauya sheƙa da tattaunawar kawance tsakanin ’yan siyasa su ɗauke hankalinsu.

    “Bari in tunatar da mu: kada mu bari sauya sheƙa da jita-jita su ɗauke mana hankali.
    Wasu mutane na sauya jam’iyya cikin sauki, suna tunanin sun san komai—alhali ba su fahimta sosai ba. Idan suna son sanin gaskiya, sai su zo su tambaye mu,” in ji shi.


    [ad_2]

    Source link

  • Kudaden Ajiya Na Asusun Nijeriya Ya Karu Zuwa Dala Biliyan 41

    [ad_1]

    A ranar 19 na watan Agustan shekarar 2025, kudaden Nijeriya na Asusun Ajiyar na kasar waje, sun karu zuwa dala biliyan 41.

    Wannan Aaron ya nuna cewa, shi ne magi yaws da aka samu tun shekarar 2021.

    Bayanin hakan na kunshe ne, a cikin wasu alkaluman da Babban Bankin Nijeriya CBN ya fitar.

    Bisa wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, hakan ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da Asusun Anita na Nijeriya ya samu karuwa tun daga watan Disambar shekarar 2021.

    Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, a watan Agusta Asusun ya ci gaba da karuwa wanda daga watan aka samu kimanin dala biliyan 1.46 zuwa yau daga dala biliyan 39.54 a ranar daya 19 ga watan Agustar shekarar 2025, suka karu zuwa i dala biliyan 41.00.

    Wannan ya nuna yadda karuwar Asusun ta kai zuwa kaso 3.69 a kasa da makwanni uku, da suka gabata.

    Bugu da karu, Asusun ya samu wannan karuwar ce, saboda yawan shigowar kudaden musaya na waje cikin kasar da kuma karin da aka samu, a bangren danyen Mai.

    A cewar wasu alkaluma da Babban Bankin Nijeriya CBN ya fitar, sun bayyana cewa, a Ragnar data ga watan Agustan shekarar 2025, kudaden da ke a cikin Asusun, sun kai yawan dala biliyan 39.3 wadanda kuma a ranar 6 ga watan Agustan suka kai yawan dala biliyan 40.2 kafin kaiwarsu, zuwa wannan a dad in na yanzu.

    Wasu masu yin fashin baki kan tattalin arziki, sun danganta samun wannan karin kan sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da yi ne, a fannin tattalin arzikin kasar.

    Babban sashen da ya fi amfana shi ne, bangaren Asusun Ajiyar kudade na kasar da ke a kasar waje wanda ya kai yawan dala biliyan 40 kusan za a iya cewa, a cikin mako biyu, kafin Asusun ya wannan yawan a dad in na yanzu.

    Karin da aka samu na Asusun Ajiya na kasar da ke a ketare, ya buna cewa, ya kai dala biliyan 39.3 a ranar daya ga watan Agusta wanda kuma a ranar Takwas ga watan Agusta, ya kai dala biliyan 39.5 inda kuma a ranar shida ga watan Agusta ya kai dala biliyan 40.2 sai kuma a ranar sha daya ga watan Agusta ya kai dala biliyan 40.65 kafin kuma ya karu zuwa dala biliyan 40.72 a ranar sha uku ga watan Agusta.

    Idan za a iya tunawa, Asusun ya fara ne da kafar dama a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2024, inda kudaden Asusun suka kai dala biliyan 40.88.

    Daga watan Janairu zuwa na Yuni, Assusun ya ragu dala biliyan 37 zuwa dala biliyan 39.

    Alalmisali, Asusun na kasar wajen na kasar a farkon watan Yuli ya kasance ya tsaya kan dala biliyan 37.28 kafin ya kara karuwa zuwa matakin da yake na yanzu.

    Karin karuwar Asusun ta kai ta zama da dala biliyan uku wanda hakan ya nuna cewa, ta kai ta kimanin kaso takwas a cikin watan.

    Bugu da kari, wannan karuwar da Asusun Ajiya na waje na kasar ya samu wands a yanzu ya kai dala biliyan 41 tun bayan wanda kasar ta samu a shekarar 2021.

    Wannan karuwar ta Asusun ta kuma nuna cewa, ta hairs wadda aka samu a shekarar 2022 zuwa shekarar 2023, wadda ta kai ta dala biliyan 38.

    Bugu da karu, baya ga karuwar Asusun Ajiya na kasar waje, ita Naira ta kara samun daraja inda kuma hauhawan farashin kaya a kasar ya ragu wanda a watan Yuli ya kai kaso 21.88.

    Wasu alkaluma da Hukumar Kula da Kiddiga ta kasa NBS ta fitar, sun nuna cewa, a watan Yuli an samu raguwa, idan aka kwatanta da kaso 22.22 da aka samu a watan Yuni.

    Hakazalika, wani rahoton baya bayan nan, da Hukumar Kula da Farashin Kaya ta fitar sun nuna cewa, a watan Yuli sun kai kaso 0.34, wanda hakan ya nuna cewa, sun kai kasa da kaso 11.52 a watan Yuni kuma kasa da kaso 33.40 da aka samu a watan Yuli.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Katsina Za Ta Sayo Babura 700 Da Motoci 20 Don Samar Da Tsaro

    [ad_1]

    Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da sayen babura 700 da kuma motocin Hilux guda 20 a matsayin sabon mataki na yaƙi da ta’addanci, satar mutane da sauran ayyukan laifi a faɗin jihar.

    Wannan amincewa ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 12 da aka gudanar a gidan gwamnati, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda.

    Kwamishinan Tsaron cikin gida Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa, ya shaida wa manema labarai bayan taron cewa, matsalar yanayin ƙasa a Katsina na daga cikin dalilan da suka sa aka yanke shawarar sayen baburan, domin akwai ƙauyuka da dama da motoci ba sa iya isa.

    Ya ce gwamnati ta ɗauki tsaro da muhimmanci a matsayin abu na farko, na biyu da kuma na uku, tare da tabbatar da cewa za ta tunkari matsalar tsaro gaba ɗaya. Haka kuma, an amince da sayen kayan aikin tsaro na zamani da za su tallafa wa rundunar Katsina State Styesat Corps tare da haɗin gwuiwar DSS da sauran hukumomin tsaro.

    Dakta Danmusa ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da sayen motocin bindiga masu ƙarfi guda takwas na Toyota Land Cruiser (Buffalo) domin ƙara karfin runduna a yankunan da suka fi fama da hare-haren ƴan bindiga. Ya roƙi al’umma da su ci gaba da tallafa wa gwamnati ta hanyar addu’o’i da haɗin kai, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar dawo da zaman lafiya na dindindin.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro

    [ad_1]

    Jam’iyyar hadaka ta ADC ta bukaci Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihohin Katsina da Zamfara sakamakon karuwar rashin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da rayuka 140 a cikin watannin biyu da suka gabata.

    A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya Sanya wa hannu a kai, jam’iyyar ta bayyana kashe-kashen a matsayin wata shaida da ke nuna cewa an samu gagarumar baraka a cikin harkokin tsaron Nijeriya, sannan ta soki gwamnatin tarayya kan kasa shawo kan lamarin.

    ADC ta yi Allah wadai kan kisan gilla da aka yi kwanan nan a Malumfashi da ke Jihar Katsina, inda aka tabbatar da cewa an harbe masallata har 30 a masallaci da kona mutum 20 da ransu da kuma gidajensu. Haka nan ta bayyana cewa an sake kashe mutum 47 a Zamfara, ciki har da mutum 38 duk da an biya kudin fansa.

    “Wannan mummunan aikin yana nuna gazawar harkokin tsoro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a karkashin wannan gwamnati ta APC. Kazalika, yana zama manuniya kan tabarbarewar rashin tsaro a kasarmu, wanda ya sa har babban jami’in tsaro na kasa ya yi kira ga ‘yan kasa su koyi kare kansu,” in ji Abdullahi.

    Jam’iyyar ta kuma caccaki Shugaba Tinubu kan burus da abubuwan da suka fi muhimmanci, ta zarge shi da mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi kasa da kasa mai makon magance rikicin da al’ummar kasar nan ke fuskanta.

    “Abin takaici ne cewa maimakon fuskantar wadannan mummunan lamuran da wahalar da suka jawo, shugaban kasa Tinubu na ci gaba da tafiya kasashen waje, yana holewa a kasashen ketare, yayin da ‘yan kasa ke mutuwa da yawa,” in ji sanarwar.

    ADC ta sake ja kunnen gwamnan jam’iyyar PDP kan gudanar da taron siyasa a Jihar Zamfara kanaki kadan da kiyan mutane masu dimbin yawa.

    “Maimakon tsayawa cikin hadin kai tare da abokin aikinsu da al’umma, sun gudanar da gangamin siyasa a garin da har yanzu ke fama da kisan gillar jama’a. Abubuwan da suka gudana a wurin taron na daukar hotunan cikin murna bai nuna cewa sun damu da kasan kiyashi da aka yi wa al’umma a jihar ba, “in ji jam’iyyar.

    Baya ga kiran saka dokar ta bacin, jam’iyyar ADC ta bukaci a sake duba tsarin tsaron kasar nan gaba daya.

    “Shawarar da babban hafsan tsaro ya bayar ga ‘yan kasa kan su kare kansu, wata alama ce da ke nuna cewa tsarin tsaron kasar nan na buktar sake sabunta shi cikin gaggawar,” in ji ta.

    Jam’iyyar ta kammala da zargin jam’iyyar APC da PDP kan fifita siyasa sama da jin dadin ‘yan Nijeriya.

    “APC da PDP ba su damu da jin dadin al’ummar Nijeriya ba. Su dai sun fi nuna sha’awarsu ga samun shugabanci a cikin harkokin siyasa, inda idanunsu ke rufewa wajen ganin irin wahalhalu da kunci da ‘yan Nijeriya ke fama da su,” in ji sanarwar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas

    [ad_1]

    Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA ta bayyana cewa, a zango mai zuwa ne, za a fara aikin dala miliyan daya na Tashar Jirgen Ruwa da ke a jihar Legas.

    A cewar Hukumar mai yuwa za a samu dan tsako kan ci gaba da aikin, saboda karancin manyan kayan aiki da za a yi aikin da su, a Tashar.

    Shugaban Hukumar ta NPA, Dakta Abubakar Dantsoho ne, ya sanar da haka a wani taro hadaka a tsakanin Cibiyar kula da fitar da kaya ta kasa da Tashar Lekki da gudana a jihar Legas.

    Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu.

    Shugaban ya kuma koka kan yadda aka shafe wadannan shekarun masu yawan gaske, ba tare da an yi masu wani gyara ba.

    Ya buga misali da kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na kasasehe kamar na Togo, Côte d’Iboire da Ghana, wanda suka kasance, Tashoshin Jiragen Ruwa da manyan Jiragen Ruwa ke sauka.

    A cewar Shugaban irin lalacewar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka yi, abu ne, da ya wuce kima, wanda hakan ya sanya, sauran Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a Afirka ta Yamma, har ta kai ga suna yin gasa na kasar nan, wajen gudanar da hada-hadar kasuwancinsu.

    “Abokan gasar mu kamar Tashoshin Jiragen Ruwa na Lome, Cotonou, Abidjan da Tema, na yin amfani da damar halin da Tashoshin Jiragen mu suke a ciki ne, suke more damar gudanar da hada-hadarsu, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Shugaban.

    “Dangane da bayaan da aka samu na duniya, Nijeriya ta kasance kasa, da ke da karfin tattalin ariziki kuma mai alumma da dama a fadin nahiyar Afirka, amma har zuwa yau, Abidjan da Lome na karbar saukar manyan Jiragen Ruwa masu yawa, fiye da wadanda suke sauka a Tashar Jiragen Ruwa ta jihar Legas, “ Acewar Dantsoho.

    Shugaban ya sanar da cewa, ya zama wajibi, mu tabbatar da mun ciki wannan gibin da ake da shi, a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.

    Ya bayyana cewa, da zarar an samar da sauran kayan aikin da suka hada da kimiyyar zamani da sauransu, Tashoshin za a samu karin damar saukar manyan Jiragen Ruwan.

    Ya kuma koka kan karancin kayan aiki na saukar Jiragen a Tashoshin, wanda hakan ya sanya, Hukumar ta NPA ke zuba sabbin kayan aikin ciki har da manyan motocin janyewa da sauransu.

    Sai dai, ya sanar da a zagon farko na shekarar 2026 ake sa ran isowar kayan zuwa cikin kasar nan

    Ya ci gaba da cewa, hakan ne ke shafar Matatar Mai ta Dangote da ke a Lekki inda ya yi nuni da cewa, Hukumar ta NPA kuma, ba ta irin kayan aikin da za su iya janyo wadannan Tankokin Man din.

    Dantsoho ya sanar da cewa, Gwamnatin Tarayya ta kafa wani waje domin samar da saukin gudanar da ayyukan Matatar Mai ta Dangote, inda aka warewa hukumomin Gwamnati guda 16 wasu gurare, a cikin harabar Hukumar NPA, wanda hakan ya bai wa NPA damar tara kudaden shiga da suka kai sama da Naira biliyan 25, tun daga watan Okutobar 2024, zuwa yau.

    Ya ce, NPA na goyon bayan sauye-sauyen da Gwamnatin ke ci gaba da yi, a fannin tattalin arzikin kasar, wanda hakjan zai janyo hankulan masu son zuba hannun jari a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar

    Shi kuwa Aminu Umar, Shugaban Cibiyar a jawabinsa na maraba a wajen taron ya jaddada cewa, kirkiro da Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa na Teku, hakan na da matukar mahimmanci a bangaren shigo da kaya daga waje da kuma fitar da su, daga cikin kasar zuwa ketare.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Yadda jami’an tsaro suka kashe ’yan ta’adda a musayar wuta 50 a Neja

    [ad_1]



    Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja.

    Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar.

    Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

    Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro.

    Ya ruwaito shaidu na cewa ’yan ta’adda kimanin 300 ɗauke da makamai ne suka yi yunƙurin kutsawa ƙauyen  a ranar Talata.

    “Sun yi nufin kai hari ne a wani sansanin Hukumar Tsaro ta DSS, amma jami’an tsaron suka mayar da martani suka kashe kimanin 50 daga cikin ’yan bindigar wasu da dama suka tsere ɗauke da raunukan harbi.

    “Al’ummar mazaɓata sun tabbatar min cewa sun ga yadda ’yan ta’addar saboda tsabar girgiza, suka riƙa sassara gawarwakin abokansu suna sanyawa a cikin buhuna, suna tafiya da su a kan baburansu.”

    A wani labari makamancin wannan kuma, ’yan bindiga sun kashe wani manomi tare da jikkata wasu a yankin Kundu da ke kusa da garin Zungeru a Ƙaramar Hukumar Rafi a ranar Alhamis.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro

    [ad_1]



    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya isa Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, domin halartar taron gwamnonin Arewa maso Gabas karo na 12 da za a gudanar gobe Asabar.

    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum  ne, zai jagoranci taron.

    Taron zai mayar da hankali ne kan batutuwan tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma hanyoyin magance matsalolin ayyukan jin-ƙai a yankin.

    Za a yi taron ne na tsawon kwanaki biyu, inda ake sa ran gwamnonin za su bayar da muhimman shawarwari da kuma cimma matsaya kan matsalolin .

    A cewar Isma’ila Uba Misilli, Daraktan Yaɗa Labarai na fadar gwamnatin Gombe, bayan taron ne za a sanar da al’umma matakan da aka cimma domin haɗa kai wajen inganta ci gaban yankin.


    [ad_2]

    Source link

  • Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Kara Azamar Bunkasa Da’a A Harkokin Jam’iyya

    [ad_1]

    Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azamar inganta da’a a harkokin jam’iyya, da dorewa bisa turbar aiwatar da ka’idojin gudanar da kudurorin nan takwas, na shugabancin jam’iyyar kwaminis game da inganta da’a a harkokin jam’iyyar.

    Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi tsokacin ne cikin wani umarni da ya bayar, ga wani taron tattaunawa don kara gina jam’iyyar kwaminis a yau Jumma’a a nan birnin Beijing. (Saminu Alhassan)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link