Category: Latest News

  • Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci

    [ad_1]

    Sarkin Musulmi, Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi gargadin cewa adalci a Nijeriya yana kara zama “kayan sayarwa,” inda talakawa ke kara zama saniyar ware wadanda ake zalunta, yayin da masu kudi kuma suka fi karfin hukunci.

    Sarkin, wanda ya kasance bako na musamman a Taron Kungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) na Shekara-shekara a Enugu a ranar Lahadi, ya yi gargadin cewa cin hanci da rashin daidaito suna lalata amincin tsarin shari’a.

    “Yau adalci yana kara zama kayan sayarwa, kuma talakawa suna zama wadanda ake zalunta ta irin wannan rashin adalci, yayin da masu kudi ke aikata duk wani laifi suna yawo a titi ba tare da hukunci ba,” in ji shi.

    Ya bayyana godiya ga NBA bisa zabar taken taron ‘Tsaya da Kafarka,’ yana mai cewa ya yi daidai da bukatar lauyoyi su cika da aikinsu a matsayinsu na kwararru.

    A cewarsa, dole ne a ci gaba da jajircewa wajen kare bin doka domin tabbatar da adalci, daukar nauyi, da daidaito a gaban doka.

    ‘Kun kuduri aniyar kiyaye manyan ka’idojin bin doka domin tabbatar da cewa kowa, har da masu mulki, suna karkashin doka kuma ana iya daukar mataki a kansu. Idan muka yi haka, to mun magance tushen matsalar mulki a wannan kasa,’ in ji shi.

    Sarkin Musulmi ya jaddada cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiyar al’umma, kuma dole doka kullum ta kasance mai nufin cimma adalci a matsayin babbar manufarta.

    Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da wannan taro wajen tattauna muhimman batutuwan da suke tsara makomar Nijeriya.”

    “Ya ce, ‘Ina fatan wannan taro zai ba ku damar tattauna batutuwan da suka shafi makomar al’ummarmu.

    Abubuwa uku ne manya: Ci gaba da kokari wajen gyaran dokoki domin a hankali a kawar da tasirin mulkin mallaka a cikin dokokinmu tare da kusantar da su da kimominmu, al’adu da tarihimmu; magance batun adalcin zamantakewa domin rage gibin rashin daidaito tare da karfafa hadin kai; da kuma inganta samun damar zuwa kotu, musamman la’akari da tsadar shari’a da kuma yadda marasa karfi da masu rauni ake barinsu a baya.’

    Ya yi tir da matsalar da Nijeriya ke fama da ita ta rashin aiwatar da manufofi yadda ya kamata duk da kasancewar manufofin “masu kyau kwarai.”

    Doka da ilimi ba za a iya raba su ba.

    A fannin sanin doka akwai sanin kima, kuma adalci na daya daga cikin manyan kimomin da doka ya kamata ta cimma,’ in ji Sarkin Musulmi wanda ya bayyana haka ga mahalarta taron, ciki kuwa har da shugaban jam’iyyar hamayya na Afirka ta Kudu, Julius Malema.”

    Ra’ayin Lauya, da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Bambanta Kan Maganar Sarkin Musulmi Game Da Alkalancin Nijeriya

    Yayin da Nijeriya ke ci gaba da fama da tsarin shari’a mara inganci wanda ke bayyana gazawar kotuna wajen tabbatar da adalci, boye shaida, halayyar rashin da’a ta masu shari’a, cin hanci da rashawa, da tsoma bakin siyasa cikin tsarin shari’ar kasa, jama’a da dama sun nuna rashin yabonsu ga tsarin.

    Wannan ra’ayi ne Sarkin Musulmi na Sakkwato, Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya jaddada a Taron Koli na Kungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) da aka gudanar a Enugu ranar Lahadi, inda ya yi gargadin cewa adalci a Nijeriya na kara zama ‘kayan ciniki,’ inda talakawa ke zama wadanda ake zalunta, kuma masu kudi ke fin karfin doka.”

    Yayin da yake mayar da martani ga maganar wannan girmamaccen sarki, wani malamin lauya, Dr. Wahab Shittu (SAN), ya bayyana furucin Sultan a matsayin abin takaici kwarai kuma rashin adalci ga alkalan da ke jajircewa da aiki tukuru da kuma gaba daya bangaren shari’a.

    Dr. Shittu ya ce, “Ikirarin cewa a Nijeriya ana iya sayen adalci wata fahimta ce kawai, ba gaskiya ba. Wannan kuwa rashin adalcin fahimta ne da kuma maganganun da ake ta yi a teburin shan shayi.”

    “Ina ganin masu ruwa da tsaki a harkar gudanar da shari’a suna da babban alhaki na canza wannan labari. Ya kamata a samu adalci bisa cancantar shari’ar da aka gabatar, ba bisa wanda ya fi bayar da kud ba.”

    Haka kuma, yayin da yake mayar da martani kan maganar Sultan Sa’ad Abubakar cewa adalci yana zama abin saye a Nijeriya, Kwamared Bankole Solomon (esk), shugaban Kungiyoyin Farar Hula (CSOs) da Kungiyoyin Goyon Bayan Dimokuradiyya a Jihar Ogun, ya yaba wa wannan fitaccen sarki bisa karfin gwiwar da ya nuna na fadin gaskiya kan wannan batu.

    Bankole ya ce, “Abin takaici ne kwarai cewa mun kai ga shiga wannan mummunan hali a kasarmu.

    “Ina tare da Sultan wajen cewa adalci yanzu na mai bayar da kudi ne, ko kuma in ce adalci a Nijeriya ya zama kayan sayarwa, domin idan ka ga abubuwan da ke faruwa, sai ka tausaya wa wannan kasa.

    “Ina fada wa mutane cewa bisa ga abubuwan da muka gani da CSOs, ma ya fi sauki, arha da adalci akan bayar da cin hanci a matakin ‘yansanda; ko a ofishin ‘yansanda, ko a Area Command, ko kuma a hedikwatar jiha, fiye da a kotu, domin makudan kudi ake nema a kan saukakan matakai a kotu.”

    “Wasu mutane za su saurare ka, su ji maganarka, kuma watakila su yi maka shaguben cewa ai wani ya bayar da kudin beli. Amma da za ka san irin abin da ake karba domin kammala wannan belin a kotu, za ka yi wa kasar nan kuka.”

    Jeka Kotu, Maza Ka Garzaya Kotu

    “Akwai wasu shari’o’in da idan aka fara su, wani lokaci za ka gaskata cewa lallai ba su da kyau, amma daga karshe idan ka ga sakamakon, za ka gane cewa tabbas wannan ba abin da ake tsammani daga bangaren shari’a ba ne. Shi ya sa yau a kasar nan ya zama magana ta kowa idan ka ji ana cewa:” “Jeka kotu”! Idan an sace maka dukiyarka, “jeka kotu”! Duk wanda ya kai maka hari, “je kotu”! Idan ka yi zargi ko ka yi hasashen dan siyasa ya sace dukiyar kasa, “jeka kotu”! Du kana fadar haka ne saboda sun san za su iya yin yadda suka ga dama idan shari’ar ta kai kotu.

    Babu attajiri a gidan yari, talakawa kadai ake samu

    “Don haka, ina son in yarda da Sultan cewa adalci yana zama kayan sayarwa; ta hanyar wanda ka sani da kuma yawan kudin da kake da shi! Kuma wannan shi ne abin da ake tattaunawa a yau, domin idan ka ziyarci Gidajen Gyaran Hali a fadin kasar nan, da wuya ka ga attajiri; da wuya ka ga babban dan siyasa; abin da za ka gani kawai talakawa ne wadanda saboda wani dalili ko wani ba su samu hanyar tsira ba, ko kuma ba su da hanya, ko rashin yin abu, ko dabaru da za su ba su damar sayen hanyar da za su fita.”

    “A takaice, ba damuwar Sultan da sarakunan gargajiya kadai ba ce; har ma da bangaren CSOs ba su gamsu da abin da ke faruwa ba. Muna ziyartar kotuna muna sauraron labarai, kuma muna ganin wasu mutane da muka sani wadanda shari’unsu a fili suke cewa take hakkin su aka tauye, amma idan ka shiga kotu, yawanci hukuncin da za ka gani abin shakku ne.”

    “Don haka, ba tare da boye magana ba, na yarda kuma na amince gaba daya da furucin Sultan Sa’ad Abubakar cewa adalci a wannan duniya kayan sayarwa ne tsantsa.”

    Lauyoyi Sun Yi Kira da A Yi Hattara

    Wasu lauyoyi sun nemi a dauki matakin gaskiya daga bangaren shari’a, inda suka yi gargadin cewa idanun kowa na kan bangaren shari’a domin ganin an yi adalci ba tare da tsoro ko son zuciya ba.

    A cewarsu, ya zama dole harkar lauya ta sake samun girmamawar ‘yan Nijeriya ta hanyar yin abin da ya dace koyaushe.

    Haka kuma sun yi kira da a yi hattara game da maganganun da ba su da tushe wadanda nufin su shi ne bata sunan bangaren shari’a.

    Bangaren Shari’a Bai Yi Muni Kamar Yadda Ake Ambatawa Ba

    Lauyan kundin tsarin mulki, Farfesa Isah Awo, ya ce Sultan na iya kuskure. Ya ce bangaren shari’a ba ya da muni kamar yadda jama’a ke ambatawa.

    “Duk da cewa zan yarda cewa wasu shari’o’i da ke fitowa daga kotunmu na iya samun rashin daidaito, wannan kananan abu ne sosai don a iya cewa ana iya sayan adalci.

    “Ban yarda cewa ana iya sayen adalci ba, kuma bangaren shari’a na Nijeriya bai kai kasa haka ba.

    “Akwai lokuta da bangaren shari’a zai iya gazawa; zai iya gazawa kan yadda mutane ke tsammani, amma har yanzu bai lalace kamar yadda ake bayyana shi ba.”

    Kada mu tsoratar da masu zuba jari na kasashen waje

    A nasa bangare, wani lauya dake Abuja, Barrister Innocent Amokade, ya yi gargadi kan lalata bangaren shari’a.

    Ya ce irin wadannan maganganun na iya rage amincewar masu zuba jari na kasashen waje a kasar.

    Ya ce idan ‘yan Nijeriya ba su yarda da tsarin kasarsu ba, me kuke so ‘yan kasashen waje su yi?

    “Muna bukatar mu yarda da tsarinmu domin hadari ne a sa ‘yan kasashen waje, musamman masu zuba jari, su yi imani cewa bangaren shari’armu ba mai zaman kansa ba ne. Wannan zai rage musu amincewa da ikonmu na yin adalci.”

    Sarkin Sokoto, Mai Girma, Dr. Sa’ad Abubakar III, ne ya jagoranci bikin bude taron. Julius Malema, jagora mai jan hankali na kungiyar Economic Freedom Fighters ta Afirka ta Kudu kuma mamba na majalisar dokokin kasa, shi ne ya gabatar da jawabin babban mai jawabi.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya

    [ad_1]

    A cikin wannan hali na matsin tattalin arziki, gwamnatin tarayya na kokarin aiwatar da wasu sauye-sauye a bangaren makamashi, ciki har da cire tallafin wutar lantarki.

    Jaridarmu ta LEADERSHIP ta ruwaito cewa Ministan Kudi, Wale Edun, ya sanar da haka bayan wani taron majalisar ministoci kwanan nan, inda ya ce shirin sake fasalin bashi zai kammala cikin ‘yan makonni.

    Shirin ya kuma hada da karin kudin wutar lantarki ga manyan masu amfani, matakan da gwamnatin tarayya ke sa ran za ta samu fiye da Naira 1 tiriliyan a kowace shekara.

    A cewar Edun, gwamnati za ta gabatar da tsarin pay-as-you-go ga masu amfani da wutar lantarki domin kawo karshen tallafin gwamnati a wannan bangare.

    Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati.

    Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar.

    Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi.

    Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar lantarki da yin hadin baki.

    Ya ce: “Akwai haramtacciyar alaka tsakaninsu. Wannan yana nuna muku girman lalacewa da rikice-rikicen da ke cikin tsarin,” in ji shi.

    Upah ya soki tsarin kebancewar harkar wutar lantarki, yana mai cewa yana bukatar a sake duba shi, ko ma a soke shi gaba daya.

    Ya nuna cewa in ban da cin hanci da rashawa da gazawa da babu abin da gwamnati za ta nuna, yana mai cewa rabon kudaden da gwamnati ta yi zuwa yanzu sun fi na lokacin NEPA, amma babu wani ci gaba mai ma’ana a harkar samar da wutar lantarki.

    Ya bayyana hujjar cewa babu daya daga cikin tallafin da ya nuna samun ingantacciyar wutar lantarki, yayin da hukumomin bangaren wutar har yanzu suke ikirarin cewa gwamnati tana da bashi, abin da ya haifar da shakku game da kwangilolin da aka sanya hannu da kuma sahihancinsu.

    Upah ya yi rantsuwa cewa NLC za ta ci gaba da shiri da kuma daukar mataki ta hanyar hukumomin da suka dace, domin ta ba da amsa yadda ya kamata idan matakan gwamnati na cire tallafi suka tabbata.

    “Majalisar ta yi iya kokarinta wajen fadakar da gwamnati da hukumominta masu dacewa kan abin da ya kamata a yi, sannan muka bi shi da zanga-zangar tituna lokacin da ba su yi abin da ya dace ba.

    “Duk da haka, Majalisar ba ta da niyyar yin watsi da batun. Hukumomin da suka dace. Majalisar za su hadu su kuma mayar da martani idan gwamnati ta dauki mataki,” in ji Upah.

    Kungiyar kwadago ta jawo hankalin gwamnatin tarayya kan rahoton gwamnatin Amurka da ya nuna cewa mafi karancin albashi na Naira 70,000 ba zai wadatar kan fitar da miliyoyin ‘yan kasa daga talauci ba, tana mai kawo misalai da karancin iya aiwatar da tsaro tare da rushewar darajar Naira.

    A cikin Rahotannin Kasashen 2024 kan Hanyoyin ‘Yancin Dan Adam, da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar a ranar 12 ga Agusta, 2025, an bayyana cewa mafi karancin albashin Nijeriya, wanda darajarsa yanzu ke kusan Dala 47.90 a kowane wata, ya fadi kasa da matakin kudin shiga.

    “Dokar Gyaran Mafi Karancin Albashi ta 2024 ta ninka mafi karancin albashi zuwa Naira 70,000 (Dala 47.90) a wata. Duk da karin, faduwar darajar kudi ta sanya mafi karancin albashi bai fi matakin kudin da zai jefa mutane cikin talauci ba,” in ji rahoton.

    Rahoton ya kara bayyana cewa aiwatar da dokar albashi a fadin kasar na da rauni, inda ma’aikata da dama ba su cikin wadanda dokar ta shafa.

    “Dokar ta tanadi mafi karancin albashi na kasa ga dukkan ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ke da ma’aikata guda 25 ko fiye haka, banda ma’aikatan noma da na yanayi, da wadanda ke aiki da kwangila ko kwamitoci, da sauransu.”

    “Yawancin masu aiki suna da kasa da ma’aikata 25, don haka mafi yawan ma’aikata ba su shiga cikin wadanda dokar ta shafa ba. Wasu jihohi ma sun ki aiwatar da dokar mafi karancin albashi, suna kiran karancin kudi a matsayin dalili,” in ji gwamnatin Amurka.

    Upah ya kara da cewa, har ma gwamnatocin kasashen waje sun san da matsanancin halin talauci a cikin kasar.

    Amurka, a cikin rahoton, ta kuma lura cewa ko da yake dokar ta wajabta awanni 40 na aiki a mako, hutun shekara na makonni biyu zuwa hudu, da biyan kudin karin aiki da na hutu, har yanzu akwai gibi wajen fayyace karin albashi da karin lokaci.

    “Dokar ta haramta yawan tilasta karin aiki ga ma’aikatan farar hula na gwamnati,” in ji rahoton.

    Sai dai rahoton Amurka ya soki karfin gwamnatin Nijeriya wajen aiwatar da ka’idodin aiki.

    “Gwamnatin tarayya ba ta cika aiwatar da mafi karancin albashi, biyan karin lokaci, da dokokin tsaron muhalli da lafiya na wuraren aiki (OSH) ba. Hukuncin da ake sanyawa kankani ne kuma ba su yi daidai da sauran laifuka kamar almundahana ba, kuma an samu dadadden lokaci ana iya cewa ba a cika amfani da su ba,” in ji rahoton.

    Tinubu ya kamata ya rage wa ‘yan Nijeriya nauyi, ba ya kara musu ba – Secondus, Abdullahi

    A nasa bangaren, tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Prince Uche Secondus, ya roki Shugaban Kasa da ya sake tunani kan shirin cire tallafin wutar lantarki

    ‘Wannan ba lokacin yin wasa da walwalar ‘yan Nijeriya ba ne. ‘Yan Nijeriya sun dauriya sosai a karkashin wannan gwamnati. Shugaban kasa bai kamata ya kara musu wata azaba ba.

    ‘‘Maimakon ya kara musu nauyi, ina ganin ya kamata shugaban kasa ya yi tunanin yadda zai rage musu nauyin,’’ in ji shi.

    Wani masanin tattalin arziki, Gabriel Adewuyi, ya ce ko da yake tallafi ba shi ne mafi alheri ga gwamnati ba, amma albashin da ma’aikata ke karba yanzu ba zai iya kara raunana kudin shiga ba.

    A cewarsa, ‘‘Mun yarda cewa tallafi watakila ba shi da kyau ga tattalin arziki, amma babu wata gwamnati a duniya da ba ta tallafa wa ‘yan kasarta ba.

    ‘‘Dukkan kasashe masu ci gaba suna tallafa wa tattalin arzikinsu ta hanyoyi daban-daban. Shugaba Bola Tinubu ya kamata ya mai da hankali wajen kara yawan samarwa da kafa masana’antu don talakawa.

    ‘‘Har ila yau, zabe na 2027 na tafe. Shin wannan shi ne lokacin da ya dace ya kara wa masu zabe radadi? Lokacin da yake yakin neman zabe shekaru uku da suka wuce, ya ce farashin man fetur zai sauka. Shin ya sauka?

    ‘‘Da zarar ya ci zabe kuma ya hau mulki, abin farko da ya yi shi ne cire tallafi ba tare da ya samar da wani abu da zai rage wa ‘yan Nijeriya tasirin hakan ba. Don Allah, ku taimaka a roke shi ya sassauta.’’

    Haka kuma, mai magana da yawun kungiyar adawa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya zargi gwamnati da rashin kula da walwalar ‘yan Nijeriya.

    Ya ce, ‘‘Ku dubi halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, amma mutanen gwamnati kamar ba su sani ba.

    ‘‘Shi ya sa suke son kara wa kansu albashi. To ku fada min, Naira 70,000 a kasuwa yanzu ya ishi ga uba mai mata daya da ‘ya’ya uku? Mene ne zai iya yi da wannan kudi?

    ‘‘Buhun shinkafa ya fi albashin mafi karancin albashi. Yanzu kuma kuna ce wa ma’aikata su daure belt dinsu don kada wandonsu ya fadio saboda rama, amma na jami’an gwamnati na tsinkewa saboda nauyi da annashuwa.

    ‘‘Walwala da tsaron al’umma su ne manyan ayyukan gwamnati. To ku fada min, shin wannan gwamnati tana samar da su? Duk wannan abin lokaci ne kawai; kwanciyar hankali zai ta zo nan gaba,’’ in ji shi.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Legas Ta Laƙume Aikin Naira Tiriliyan 3.9 Cikin Shekaru Biyun Tinubu

    [ad_1]

    Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jihar Legas ta samu amincewar ayyuka daga gwamnatin tarayya da suka kai darajar Naira tiriliyan 3.9, adadin da ya fi gaba ɗaya abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso Gabas. Wannan ya tayar da cece-kuce kan batun adalci da daidaituwar raba kuɗaɗen ci gaban ƙasa.

    Binciken ya nuna babban giɓin da ke cikin rabon kasafin ayyukan ci gaba a Nijeriya. Duk da cewa Legas kaɗai ta samu ayyuka da darajar tiriliyan 3.9, jihohin Kudu maso Gabas (N407.49bn)Arewa maso Yamma (N2.7trn), da Arewa maso Gabas (N403.98bn) sun raba jimillar tiriliyan 3.56. Yankin Kudu maso Yamma, wanda Legas ke ciki, ya fi kowa samu da jimillar tiriliyan 5.97, da suka haɗa manyan ayyuka irin su Lagos-Calabar Coastal Highway da gyaran filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ya kai Naira biliyan 712.

    Sai dai gwamnatin tarayya ta ƙaryata zargin nuna bambanci. Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, ya bayyana cewa shirin Sabunta Kasashen Duniya na Tinubu yana tafiya bisa tsarin adalci, inda ya nuna ayyuka irin su hanyar Sokoto-Badagry da jiragen ƙasa a Kano da Kaduna a matsayin hujja na aikin “ci gaban ƙasa baki ɗaya.”

    Amma masu suka na ganin lambobin sun tabbatar da akasin hakan. Wani Jigon PDP, Timothy Osadolorya zargi Shugaban ƙasa da yin mulkin ƙabilanci fiye da na ƙasa baki ɗaya, yana mai cewa sauran yankuna suna samun “ragowar ci gaba.” Haka kuma, mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Auwal Rafsanjani, ya soki doka da tsarin kashe makudan kuɗaɗe ba tare da tsayayyen kasafi ba, yana mai danganta matsalar da “tsarin da ke tsotsar gumin wasu” wanda ke haddasa rashin ci gaba da jin cewa ana nuna wariya.

    Wannan bincike ya sake fito da tsohon ƙalubale a tsarin mulkin Nijeriya: yadda za a daidaita muhimmancin raya cibiyoyin tattalin arziƙi irin su Legas da kuma wajabcin adalci wajen rabon arzikin ƙasa.

    Yayin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da tura manyan ayyukan ci gaba zuwa Legas, tambaya a nan shi ne: shin za a ji daɗin “Sabunta bege” daidai da yadda ake ji a bakin tekun Legas a ƙauyukan Arewa maso Gabas?




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike

    [ad_1]



    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare.

    Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar.

    Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor.

    Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata.

    Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya zama dole, domin idan ba a yi shi ba, babu wanda zai shugabanci matakin ƙananan hukumomi bayan ka8rewar dokar ta-ɓaci.

    Wike ya ce: “Ranar 18 ga watan Satumba dokar ta-ɓaci za ta ƙare, kuma gwamna da ’yan majalisa za su koma bakin aikinsu.

    “Kotun Ƙoli ta soke zaɓen da ya gabata, don haka idan ba a gudanar da wannan zaɓen ba, hakan na nufin babu shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.”

    Ya kuma ƙara da cewa kayan zaɓe sun isa a kan lokaci, kuma jama’a suna kada ƙuri’arsu cikin kwanciyar hankali.


    [ad_2]

    Source link

  • A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn

    [ad_1]



    Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa.

    Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka haɗa da jihohi 18.

    Rahoton binciken da wakilanmu suka gudanar ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 3.9 a jihar Legas.

    A cewar rahoton, cikin lokaci guda, FEC, wadda Shugaban Ƙasar ke jagoranta, ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 5.97 ga Kudu maso Yamma, tiriliyan 2.41 ga Kudu maso Kudu, biliyan 407.49 ga Kudu maso Gabas, tiriliyan 1.15 ga Arewa ta Tsakiya (da Abuja), tiriliyan 2.7 ga Arewa maso Yamma, da biliyan 403.98 ga Arewa maso Gabas.

    Haka kuma an ware naira tiriliyan 2.70 don manyan hanyoyi da za su ratsa yankuna daban-daban, ba tare da bayani kan takamaiman kuɗin kowanne ba. Wannan ya sa jimillar ayyukan da FEC ta amince da su ta kai Naira Turkiya 15.79.

    Minista ya kare Shugaba Tinubu

    Wasu ƙungiyoyin da ke kafofin sada zumunta da kuma Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) sun ta da ƙarar cewa Gwamnatin Tinubu ta fi bayar da filin ayyuka ga yankin Kudu, musamman mahaifasrsa Jihar Legas.

    Sai dai Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce ba haka lamarin yake ba. “Rarraba ayyuka a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana gudana bisa adalci ga dukkan jihohi. Babu wani yanki da aka ba wa fifiko fiye da wani,” in ji shi.

    Ya ce gwamnatin ta kuma samar da kuɗaɗen gine-gine na layin dogo na Naira biliyan 150 a Jihar Kano da kuma biliyan 100 a Jihar Kaduna, kana aka ware Naira biliyan 712 don sabunta tashar jiragen sama ta Murtala Muhammed a Legas.

    Manyan ayyukan da aka ware wa Legas

    Kuɗaɗe da kuma ayyukan da gwamnatin Tinubu ta ware wa Jihar Legas a shekara biyu da suka gabata sun haɗa da:

    – Naira tiriliyan 1.6: Domin gina titin Legas–Kalaba mai tsawon kilomita 55.

    Naira biliyan 712: Domin Sabunta Tashar Jirgin Sama ta Murtala Muhammed.

    – Naira biliyan 359: Na gina gadoji da gyaran hanyar Carter Bridges.

    – Naira biliyan 176.49: Domin gyaran bakin teku a Ebute-Ero/Marina.

    – Naira biliyan 49.9: Katangar tsaro da kuma na’urorin CCTV a filin jirgin Legas.

    Akwai kuma ayyuka da dama a sauran jihohin Kudu maso Yamma, ciki har da Ogun, Ekiti da Ondo, waɗanda darajarsu ta kai tiriliyan 1.65 da sauran biliyoyi da dama.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa

    [ad_1]



    Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas, ya shirya wa Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas inda ya shirya musu ƙasaitaccen biki da liyafar dare a Jalingo, a gabanin taron gwamnonin da za a gudanar yau Asabar.

    An gudanar da liyafar ne a daren Juma’a a babban ɗakin fadar gwamnati, inda aka nuna raye raye na al’adu daga kungiyoyin gargajiya na Taraba da sauran jihohin yankin.

    A jawabinsa, Gwamna Kefas ya bayyana cewa haɗin kan Arewa maso Gabas na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ingantattun ababen more rayuwa.

    Ya kafa da cewa taron gwamnonin na bayar da dama ta musamman don tsara manufofi da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin.

    A cewar sanarwar da mai magana da yawun fadar gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya nanata kudirin gwamnonin na yin aiki tare domin ci gaban Arewa maso Gabas baki ɗaya.

    Shugaban taron, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jinjinawa Gwamna Kefas bisa shirya wannan liyafa, yana mai cewa baje kolin al’adu da zumunci za su ƙara karfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin jihohin yankin.


    [ad_2]

    Source link

  • ‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi

    [ad_1]

    Rundunar ‘Yansanda Jihar Kebbi ta yi nasarar hana wani yunkurin sace mutum, inda ta ceto wani da aka yi garkuwa da shi daga hannun ‘yan bindiga a Kauyen Kesan, Karamar Hukumar Shanga.

    Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana a cikin wata sanarwa ranar Lahadi cewa lamarin ya faru da safiyar Asabar lokacin da ‘yan bindiga suka afka cikin al’umma suka sace wani matashi mai shekara 25, Abdulmumini Alhaji Ahmadu.

    “Bayan samun kiran gaggawa, Dibisional Police Officer na Shanga ya hanzarta hada tawagar ‘yansanda da ‘yan sa-kai, inda suka bi sahun masu garkuwa da mutane har cikin daji.

    “A yayin aikin ceto, wanda aka sace din ya sami raunin harbin bindiga a kafarsa ta hagu bayan ‘yan ta’addan sun bude wuta lokacin da suke kokarin tserewa,” in ji sanarwar.

    An garzaya da wanda aka ceto zuwa asibiti, kuma a halin yanzu yana samun sauki.

    Kwamishinan ‘Yansanda, Bello M. Sani, ya yaba wa jarumtar jami’an da ‘yan sa-kai bisa saurin daukar mataki, tare da sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da yaki da miyagun laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Jihar Kebbi.

    “Wannan aikin ceto ya nuna jajircewarmu wajen kawar da miyagun laifuka a jihar. Ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da tsaron kowace al’umma,” in ji Sani.

    Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu fadakarwa tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci, domin hana aikata laifuka.

    Kwamishinan ya jaddada cewa tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, yana mai bayyana cewa hadin kai mai karfi tsakanin jami’an tsaro da jama’a shi ne ginshiki wajen kawo karshen ta’addanci da sauran laifukan da ke barazana ga zaman lafiya a jihar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi

    [ad_1]

    Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum hudu da ake zargin ‘yan fashi ne daga cikin wata kungiya mai mutane 20 da ta kai farmaki unguwannin Madina da Fadaman Mada a jihar a ranar 16 ga Agusta, 2025.

    An samu ruwait cewa miyagun mutanen, dauke da bindigogi, adduna, wukake da sanduna, sun afka wa unguwannin da sassafe, inda suka kwace wa akalla mutum 10 kayayyaki masu daraja, ciki har da wayoyin hannu guda 14, talabijin guda biyu, kaya na maza guda biyu da kuma kudi Naira 100,000.

    Mai magana da yawun rundunar, Ahmed Wakil, ya tabbatar da cafke mutanen a cikin wata sanarwa da ya raba wa wakilinmu a ranar Asabar.

    Ya bayyana cewa, “A ranar 16/08/2025, da misalin karfe 03:20 na dare, an samu kiran gaggawa daga wani da ba a bayyana sunansa ba, yana sanar da cewa tsakanin karfe 02:00 da 03:00 na dare, wata kungiyar ‘yan fashi kusan 20 dauke da makamai sun afka unguwar Madina da bayan tsohon makabarta a unguwar Fadaman Mada, inda suka shiga gidaje da dama suka yi wa mazauna sata tare da kwace musu kayayyaki masu daraja.”

    Wakil ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga sashen C Dibision, karkashin jagorancin Dibisional Police Officer, sun hanzarta zuwa wurin tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai. Da zarar ‘yan fashin suka hango jami’an, sai suka tsere suka bar wasu daga cikin kayayyakin da suka sace.

    “A nan gaba kadan, da misalin karfe 05:03 na dare a wannan rana, jami’an leken asiri da ke aikin sintiri suka kama daya daga cikin barayin, Ahmed Hassan, mai shekara 20, dan unguwar Tirwun, Bauchi, yayin da yake yawo a Warinje Hills da wayar hannu ta Gionee da aka kwace a hannunsa,” in ji shi.

    A cewar sanarwar, bayanin da Hassan ya bayar ya taimaka wajen cafke sauran mutum uku: Ismail Isah mai shekara 18 (wanda aka fi sani da Masha), Uzaifa Abubakar mai shekara 19 (wanda aka fi sani da Damo), da kuma Abdulhamid Idris mai shekara 20.

    Kayan shaidar da aka kwato sun hada da bindigar kera gida kirar rebolber, harsashi daya na 7.62mm, wuka, bindigar gida gajera (Dane gun), adduna guda biyu, da fitila.

    “A lokacin binciken da ake yi musu, wadanda ake zargin sun amsa cewa su ne ke da alhakin wasu ayyukan fashi da makami daban-daban a cikin Birnin Bauchi. Ana ci gaba da kokari don bin diddigin sauran abokan harkarsu da kama su. Bayan kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Wakil.

    Wannan cigaban ya biyo bayan karin matakan da ake dauka wajen yaki da aikata laifuka a jihar. A baya-bayan nan, Kwamishinan ‘Yan Sanda, Sani Omolori-Aliyu, ya bayyana cewa an kama mutane 748 da ake zargi da hannu a cikin laifuka 394 a Bauchi cikin watanni takwas da suka gabata.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Editan BBC Hausa ya magantu kan zargin musguna wa ma’aikciya

    [ad_1]



    Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ce zargin cin zarafi a wurin aiki da ake yi masa ba su da tushe.

    Lamarin ya samo asali ne bayan wata tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa, Halima Umar Saleh, a yayin wata tattaunawa da tashar Arewa24 ta bayyana cewa ta fuskanci musgunawa a lokacin aikin ta, kodayake ba ta ambaci sunan editan da ya yi mata hakan ba.

    A cikin bidiyon, Halima ta ce ta sha wahala a lokacin da take aiki a sashen, tana mai cewa wani babban jami’i ya nuna mata ƙiyayya ba tare da wani dalili ba, abin da ya sa ta shiga damuwa ta kan yi kuka akai-akai.

    Ta bayyana cewa ta sha barazanar korar aiki duk da cewa ba ta aikata wani laifi ba, har ma ya yaba mata cewa tana yin aikinta yadda ya kamata.

    Bidiyon ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka buƙaci a gudanar da bincike kai tsaye.

    Amma Aliyu Tanko, wanda mutane da dama suka nuna a matsayin wanda ake zargi, ya ce lamarin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa siyasar ofis ce kawai ta haddasa haka.

    A lokacin da wakilinmu ya tuntuɓe shi, ya ƙi yin ƙarin bayani kan rahotannin da ke cewa an dakatar da shi daga aiki. Amma dai ya kuma tabbatar da cewa ya miƙa takardar murabus, sai dai har yanzu bai samu amsa daga mahukunta ba.

    BBC ta bayyana cewa ba ta yin tsokaci kan lamurran ma’aikata kai tsaye, amma tana daukar duk wani ƙorafi kan halayya a wurin aiki da muhimmanci.


    [ad_2]

    Source link

  • NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano

    [ad_1]

    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Jihar Kano, ta ce ta cafke wani dan shekara 29 da ake zargi da rike da kwayoyin Tramadol guda 7,000.

    Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Sadik Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Kano.

    Muhammad-Maigatari ya ce an cafke wanda ake zargin ne a ranar Asabar ta hannun jami’an hukumar da ke karkashin rundunar Kiru, a kan hanyar Zariya zuwa Kano, kusa da Kwanar Dangora, a lokacin da yake tahowa daga Legas da buhunan kwayoyin Tramadol.

    Ya bayyana cewa kwayoyin, masu nauyin kilo 4.1, an boye su a cikin wani jakar man girki mai lita 20, inda ya bayyana kama din a matsayin babban ci gaba a yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi a jihar.

    A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa da kwarewa wajen gano yadda aka boye kwayoyin.

    “Wannan lamari ya nuna jajircewar hukumar wajen katse hanyar rarraba miyagun kwayoyi da tabbatar da tsaron al’umma.”

    Ya rawaito kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da himma wajen gudanar da aikin.

    Idris-Ahmad ya kuma yaba wa shugaban hukumar NDLEA na kasa, Tsohon Birgediya-Janar mai ritaya, Mohamed Buba-Marwa, bisa goyon baya da jagoranci da yake bayarwa.

    “NDLEA a Jihar Kano ta dage wajen aiwatar da manufarta ta kawar da miyagun kwayoyi a jihar, tare da gode wa hadin kai da goyon bayan jama’a wajen cimma wannan buri,” in ji shi.

    A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa da fasaha wajen gano boyayyun kwayoyin.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link