Ban taɓa cewa zan tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba – Datti Baba-Ahmed
[ad_1]
Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Datti Baba-Ahmed, ya karyata rahotannin da ke cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
A tattaunar shi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Baba-Ahmed ya ce an yi kuskuren fassara maganarsa, yana mai jaddada cewa bai taɓa yin irin wannan maganar ba.
“Ina mai tabbatar muku, ban taɓa bayyana niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ba kwana biyu da suka wuce,” in ji shi.
A cewarsa, maganganun da ya yi kwanan nan sun takaita ne wajen sake tabbatar da kasancewarsa ɗan jam’iyyar LP, a yayin da tattaunawar siyasa ke ƙaruwa kan makomar jam’iyyar da manyan jagororinta.
Ya amince cewa kodayake akwai yiwuwar tsayawa takara a nan gaba, amma a yanzu ba a yi wata sanarwa ko yanke hukunci a kan haka ba tukuna.
Wannan bayani ya biyo bayan rahotannin da suka yadu a kafafen yada labarai da na sada zumunta da ke cewa Baba-Ahmed yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa kafin babban zaɓen baɗi.
Rahotannin dai sun jawo muhawara tsakanin magoya baya da masu sharhin siyasa, inda akasarin su suka ɗauki maganarsa a matsayin alamar sha’awa.
Yayin da yake ƙarin bayani, Baba-Ahmed ya ce: “Kwana biyu da suka wuce, abin da na yi kawai shi ne na ce har yanzu ina cikin LP. Ban taɓa bayyana niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ba, ko da yake akwai yiwuwar hakan nan gaba. Amma tabbas ban bayyana ba. Na jaddada kasancewata a LP kuma shi ne kawai.”
Ya ƙara da cewa duk wata sanarwar sha’awa za ta dogara ne da jadawalin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da tsarin cikin gida na jam’iyyar.
“Abin da na faɗa shi ne dole sai an jira jadawalin INEC da kuma lokacin da jam’iyya za ta kira mutane su nuna sha’awarsu. Ban bayyana sha’awa ba tukunna,” in ji shi.
Baba-Ahmed ya kuma soki rawar da kafafen sada zumunta ke takawa wajen yada bayanan da ba daidai ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link