APC Ta Maye Gurbin Uzodimma Da Masari A Matsayin Shugaban Kwamitin Babban Taronta Na Ƙasa
[ad_1]
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta maye gurbin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a matsayin Shugaban Kwamitin Shirya Babban Taronta na Ƙasa.
APC ta ce an yi wannan sauyi ne bayan shawarwari da shugabannin jam’iyyar.
- GORON JUMA’A
- Majalisar Ƙoli Kan Shari’ar Musulunci Ta Sake Neman A Cire Shugaban INEC
An kuma mayar da Uzodimma zuwa matsayin Ma’aji.
Jam’iyyar ta ƙara yawan mambobin kwamitin daga 73 zuwa 90.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim, an naɗa shi Mataimakin Shugaban Kwamitin na Farko, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, Mataimakin Shugaba na Biyu, yayin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ci gaba da zama Sakataren kwamitin.
Babban taron na APC zai gudana ne a ranakun 27 da 28 ga watan Maris, 2026.
[ad_2]
Source link