Jami’an tsaro sun ƙwace fasfon El-Rufa’i
[ad_1]
Jami’an tsaro sun ƙwace fasfon tafiye-tafiye na tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, jim kaɗan bayan dawowarsa Nijeriya daga Masar.
Cikin wani saƙo da mai taimaka wa tsohon gwamnan kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ya wallafa a shafinsa na X cewa a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an ƙwace fasfon ne a babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
“A yau (Alhamis) jami’an tsaro sun so su kama Nasir El-Rufai bayan dawowarsa gida daga birnin Cairo.
“El-Rufai ya ƙi bin su ba tare da an nuna masa takardar gayyata ba a hukumance, sai dai duk da haka sun ƙwace takardar fasfo ɗinsa daga hannun wani mai taimaka masa,” in ji sanarwar.
Wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda tsohon gwamnan yake magana da wasu mutane a filin jirgin, inda yake cewa “idan kuna son ku gayyace ni ku ba ni takardar gayyata.”
Tun dai a ranar Larabar da ta gabata ce El-Rufai ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya za ta iya kama shi, yana mai cewa alamu sun nuna abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan shi ne zai zama mutum na gaba da ake hari.
El-Rufai ya yi wannan zargi ne a yayin wata hira da DCL Hausa, yana mai nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin ƙaruwar barazanar siyasa ga abokan hamayya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link