NNPP Ta Yi Watsi DA Rahoton Hukuncin Amurka Kan Kwankwaso
[ad_1]
Jam’iyyar NNPP ta bayyana matuƙar mamaki kan rahotannin da ke cewa Majalisar Dokokin Amurka na nazarin wani ƙuduri mai suna Dokar Ƴancin Addini da Bin Diddigin Laifuka ta Nijeriya ta 2026 (HR 7457), inda aka ambaci jagoran jam’iyyar na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mutum ɗaya tilo da zai iya fuskantar takunkumi.
A cewar jam’iyyar, ambaton Kwankwaso tare da Ƙungiyar Miyetti Allah da wata ƙungiyar da ake kira Miyatti Allah a cikin ƙudirin, wanda ka iya haifar da hana biza da kwace kadarori, wani zagon ƙasa ne da aka shirya masa. Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya fitar ranar Laraba.
- Kwankwaso Ba Shi Ne Jagoran Jam’iyyarmu Ta NNPP A Kano Da Ƙasa Ba – NNPP
- Ka Manta Da Komai, Ka Bar Abba Ya Yi Wa Kano Aiki — Matar Ganduje Ga Kwankwaso
NNPP ta yi watsi da zargin cewa jagoranta na da hannu a keta ’yancin addini, tana mai cewa babu wata alaƙa da ke nuna yana da nasaba da tsattsauran ra’ayi ko rikice-rikicen addini a Nijeriya.
Jam’iyyar ta kuma tunatar da cewa a baya Kwankwaso ya mayar da martani a fili kan matakin da Donald Trump ya ɗauka na sake saka Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargin cin zarafin ’yancin addini, tana mai cewa ana ƙoƙarin ɓata masa suna ne ba tare da hujja ba.
[ad_2]
Source link