Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar NAHCON
[ad_1]
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON).
Wannan na cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wasiƙa domin amincewa da naɗin Ambasada Yusuf.
Sabon shugaban zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, wanda ya yi murabus a ranar Litinin biyo bayan zarge-zargen a kansa da suka shafi almundahana.
Pakistan ya yi murabus a daidai lokacin da NAHCON ke shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026.
A shekarar da ta gabata EFCC ta gayyaci Pakistan kan zargin sa da hannu wajen ɓacewar wasu biliyoyin kuɗi.
Wasiƙar ta nuna buƙatar Majalisar Dattawa ta amince da naɗin kamar yadda dokar NAHCON ta tanada.
Ambasada Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne.
Ya yi aiki a matsayin Jakadan Najeriya a ƙasar Turkiyya daga shekarar 2021 zuwa 2024.
NAHCON hukumar tarayya ce da ke da alhakin tsara da kula da harkokin Hajji da Umrah a Najeriya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link