Kasar Sin Ta Dade Tana Zama Aminiya Kuma ’Yar Uwa Ga Kasashen Afirka
A yammacin yau Talata, mataimakin shugaban hukumar watsa labarai ta ma’aikatar tsaron kasa ta Sin kuma mai magana da yawun ma’aikatar, babban kanar Jiang Bin, ya fitar da bayanai game da batutuwan da suka shafi aikin soja na baya-bayan nan.
Yayin taron, wani dan jarida ya ambaci cewa shugaban Sin Xi Jinping ya amsa wasikar wasu tsoffin sojoji na yakin ’yantar da Zimbabwe, kuma Xi yana mai jaddada cewa kasar Sin ta dade tana zama aminiya ga kasashen Afirka a cikin harkokin ’yantar da al’umma da samun ci gaba. Game da haka, babban kanar Jiang Bin ya gabatar da abubuwan da suka shafi hadin gwiwar aikin soja tsakanin Sin da Afirka.
Ya ce hadin gwiwar sojojin Sin da Afirka ya dade yana bin ka’idojin daidaito, cin gajiyar juna, da samun ci gaba tare, wanda ya cimma sakamako mai kyau a fannoni da dama kamar gina rundunar sojoji, horar da kwararru, atisayen hadin gwiwa, wanzar da zaman lafiya, yaki da ta’addanci, da kuma ba da taimakon jin kai. Dandalin zaman lafiya da tsaro na Sin da Afirka da kuma ayyukan ba da agajin kiwon lafiya ga Afirka sun zama ayyukan hadin gwiwa da suka shahara tsakanin bangarorin biyu.
Ya kara da cewa rundunar sojin kasar Sin za ta ci gaba da bin ka’idoji na gaskiya da aminci, kuma sojojin bangarorin biyu suna yin hadin gwiwa tare da kuma taimakon juna, suna aiwatar shawarwarin tsaron duniya, da kuma aiwatar da “ayyukan hadin gwiwa don kiyaye tsaro” tsakanin Sin da Afirka tare, kana da ba da gudummawa ga gina kyakkyawar makoma ta bai-daya ta Sin da Afirka a sabon zamani.(Safiyah Ma)