An Gudanar Da Bukukuwa Iri-Iri Don Maraba Da Zuwan Bikin Bazara Na Sin A Kasashe Da Dama
[ad_1]
Yayin da bikin bazara na Sin ke gabatowa, an gudanar da bukukuwa iri-iri don maraba da zuwan bikin a Vietnam, Poland, da sauran kasashen duniya.
Kwanan nan, an gudanar da bikin murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa mai jigon “Barka da sabuwar shekarar Sinawa” na shekarar 2026 da kuma bikin al’adu na murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya a kasar Najeriya.
Yayin da ake zantawa da ita a gun bikin, Judy Melifonwu, shugabar ofishin kula da dangantakar abota tsakanin Najeriya da Sin bisa manyan tsare-tsare na Najeriya, ta bayyana cewa, “Ina yi wa al’ummar Sinawa fatan alheri a bikin bazara da kuma samun nasara a ayyukansu. Ina kuma yi wa kasar Sin fatan alheri da samun wadata, kuma ina fatan abokantakar dake tsakanin Najeriya da Sin za ta kara samun kusanci.
Bugu da kari, Peru, Cuba, Sri Lanka, da sauran kasashe sun gudanar da jerin bukukuwa masu jigon “Barka da sabuwar shekarar Sinawa” don murnar bikin bazara.
A ranar 5 ga Fabrairu bisa agogon wurin, an nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na kasar Sin na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a karo na farko a makarantu da filayen wasan kwallon kankara na Kanada.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link