Majalisar Ƙoli Kan Shari’ar Musulunci Ta Sake Neman A Cire Shugaban INEC

[ad_1]

Majalisar Ƙoli kan harkokin Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake nanata kiranta na a cire Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan, tana mai cewa ba ta da amincewa da cewa zai iya gudanar da zaɓe cikin adalci a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakatare-janar na majalisar, Nafi’u Baba Ahmad, ya sanyawa hannu. Majalisar ta ce kiran da take yi ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci, sai dai da batun nagarta da cancantar shugabanci. Ta bayyana cewa sabon bayanin ya zama dole ne bayan fassarar da aka yi wa wata sanarwa da ta fitar a baya ranar 28 ga Janairu.

  • Gudunmawar Shehu Ibrahim Inyass (RTA) Ga Musulunci A Wayewar Zamani (2)
  • Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

Majalisar ta jaddada cewa ba a taɓa amfani da bambancin addini wajen amincewa ko ƙin amincewa da sakamakon zaɓe ba tun daga samun ’yancin kai a 1960. Ta ƙara da cewa daga shugabannin INEC 13 da suka gabata, Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmood Yakubu ne kaɗai musulmai, amma hakan bai taɓa haifar da ƙin amincewa da zaɓe daga musulman ƙasar ba.

A cewar majalisar, dalilin neman cire Farfesa Amupitan ya shafi wasu abubuwan da ta ce ya aikata a baya, musamman wata takarda da ya jagoranci rubutawa a 2020, wadda a cikinta ta ce ya yi kalamai masu cin mutunci ga musulman Najeriya, Arewa da kuma Usman Ɗanfodio. Majalisar ta ce takardar ta yi zargin ana yi wa kiristoci “kisan kiyashi” tare da yunƙurin danganta matsalar tsaro da jihadin Ɗanfodio, abin da ta bayyana a matsayin kuskure kuma mai tayar da zaune tsaye.

Majalisar ta ƙara da cewa har zuwa yanzu Shugaban INEC bai fito ya nesanta kansa daga waɗannan kalamai ba, tana mai jaddada cewa shugabancin hukumar zaɓe na buƙatar mutum da ke kauce wa nuna bambancin addini ko ƙabilanci. A saboda haka, majalisar ta ce ba za ta amince da duk wani zaɓe da Farfesa Amupitan zai jagoranta ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *