Tsohuwar Minista Diezani Ta Yi Zargin Rashin Adalci A Kotun Da Ke Binciken Zarginta Da Cin Hanci A Birtaniya
[ad_1]
Tsohuwar Ministar Albarkatun Mai ta Nijeriya, Diezani Alison‑Madueke, ta bayyana damuwarta kan yadda ake tafiyar da shari’ar da ake yi mata a Ƙasar Birtaniya game da zargin cin hanci da rashawa, tana mai cewa ba a yi mata adalci yadda ya kamata ba.
A cewar ta, abubuwan da ke faruwa a cikin shari’ar suna nuna rashin adalci, wanda zai iya shafar sahihancin shari’ar baki ɗaya. Diezani ta ce tana shan wahala wajen kare kanta saboda wasu abubuwan da take ganin ba sa kan bin ƙa’ida a yayin gudanar da shari’ar.
- Zargin Almundahanar ₦1.35bn: Kotun Ƙoli Za Ta Warware Taƙaddamar EFCC Da Lamiɗo
- ICPC Ta Gurfanar Da Na Hannun Daman El-Rufai A Kotu Kan Zargin Rashawar N311bn
Wannan matakin na Diezani ya jawo hankalin jama’a, musamman masu bibiyar shari’o’in manyan jami’an gwamnati a ƙasashen waje, musamman ma waɗanda suka shafi manyan kuɗaɗe da cin hanci.
A halin yanzu, shari’ar tana ci gaba da gudana a Birtaniya, yayin da Diezani da lauyoyinta ke ƙoƙarin tabbatar da cewa an yi mata adalci bisa doka da ƙa’idojin shari’a.
[ad_2]
Source link