Turji da yaransa sun kama ɗan bindigar da jagoranci yin sulhu a Katsina
Ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji da yaransa sun kama Abdu Lankai, ɗan fashin dajin da taimaka wajen kawo zaman lafiya a Ƙaramar Hukumar Jibia, a Jihar Katsina.
Sun kashe yaran Lankai bakwai sakamakon saɓani da ya ɓarke a tsakaninsu.
Wasu majiyoyi sun ce wasu daga mabiya Lankai sun jikkata, biyu kuma suna cikin mawuyacin hali a asibiti a Katsina.
Lankai ya yi ƙaurin suna a cikin ’yan fashin daji a Jihar Zamfara bayan ya amince da yarjejeniya daina kai hare-hare a Jibia.
Wannan yanki ya sanya wasu yankuna na Jihar Katsina rattaba hannu kan irin wannan yarjejeniya, domin samun zaman lafiya da daina kai hare-haren ’yan bindiga.
Rikicin ya fara ne makon da ya gabata bayan rashin jituwa tsakanin Lankai da wasu ƙungiyoyi masu biyayya ga Dogo Rabe da Black, waɗanda suka kasance abokan Bello Turji, kuma waɗanda suka ƙi amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya.
“An shirya taron don sasanta rikicin da ke tsakaninsu amma sai aka mayar da taron filin yaƙi,” in ji wata majiya.
“Ƙungiyar Rabe ta zo da mayaƙanta da yawa, inda suka farmaki mabiya Lankai, suka kashe wasu shi kuma suka kama shi da ransa.”
Turji, ya tabbatar da kama Lankai cikin wani saƙon sauti da ya fitar, inda ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu a wannan rikici.
A gefe guda kuma Turji ya gargaɗi jama’a da su nisanta kansu da shiga rikicin nasu.
“Jama’a kada suiga wannan rikici. Za a binciki Lankai, kuma za a yi masa hukunci gwargwadon sakamakon da binciken ya samar,” in ji Turji.
Shugabannin yankin sun nuna damuwa kan makomar yarjejeniyar zaman lafiya.
Yusuf Sulaiman, shugaban Kwamitin Tsaro na Jibia, ya ce: “Tun bayan da labarin ya bayyana, mazauna yankin nan na cikin fargaba.
“Muna ta yin addu’a dai yanzu saboda idan ba su warware wannan rikici ba, yarjejeniyar zaman lafiya za ta iya rushewa.”
Bashir Lawal, Sakatare Janar na Ƙungiyar Jama’a ta Jibia, ya ƙara da cewa: “Kama shi abin baƙin ciki ne. Yarjejeniyar zaman lafiya a Jibia ita ce mafi tasiri a Katsina. Muna addu’a ta ɗore.”
Masanin tsaro, Dokta Yahuza Getso, ya ce wannan al’amari na nuna matsin lamba wajen tabbatar da zaman lafiya da ’yan bindiga.
“Wannan yana nuna muhimmancin ƙwace makamai da lura da ayyukan waɗannan ƙungiyoyi domin kare zaman lafiya,” in ji shi.