Muna fama da ƙarancin masu fitowa rajistar katin zaɓe a Yobe — INEC




Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa tana fuskantar ƙarancin masu fitowa rijistar katin zaɓe zagaye na biyu da ake gudanarwa a Jihar Yobe.

Kwamishinan INEC a Yobe, Ibrahim Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa akwai babban sauyi a dabarun gudanar da aikin rijistar katin zaɓe (CVR), wanda ya haɗa da kai aikin rajistar kai tsaye zuwa gundumomin ƙananan hukumomi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa mataki na farko na aikin, wanda ya ƙare a ranar 21 ga Disamba, 2025, ya samu rajistar sabbin masu zaɓe 55,070 a cikin ƙananan hukumomi 17 na jihar.

Ya ce, “Ƙalubalen da muke fuskanta sun haɗa da lokacin noma, rashin tsaro, da kuma wahalhalun da al’umma ke ciki, waɗanda suka haifar da ƙarancin fitowar jama’a don yin rijista a zagaye na farko.

“Saboda haka ne hukumar ta amince ta tsawaita lokacin rajistar har zuwa zagaye na biyu na tsawon kwanaki 50 a faɗin Jihar Yobe.”

A cewarsa, domin tabbatar da haɗin kai da kuma bai wa dukkan ’yan ƙasa da suka cancanta damar yin rijista, hukumar ta amince da raba aikin rajista zuwa matakin unguwanni da mazaɓu.

Kwamishinan ya bayyana cewa an shirya fara sabon zagayen rijistar masu zaɓe na INEC a matakin unguwanni a ranar 2 ga Fabrairu, 2026, yayin da a makon ƙarshe na aikin za a gudanar da rajistar ne a ofisoshin ƙananan hukumomi a faɗin jihar.

Ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a jihar, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da gidajen watsa labarai, da su wayar da kan ’yan ƙasa da suka cancanta da su fito su yi rijistar zaɓen.

Alhaji Ibrahim ya roƙi al’umma da su yi amfani da wannan dama ta tsawaita lokacin rijistar, yana mai cewa ita ce za ta tabbatar da cancantar su ta zaɓar shugabanninsu a babban zaɓen 2027 da kuma bayan sa.

Ya kuma nuna damuwa kan ƙarancin karɓar katunan zaɓe na dindindin (PVCs), inda ya bayyana cewa katuna 1,100 kacal daga cikin 42,756 da aka samar tun daga watan Agusta, 2025 aka karɓa.

Kazalika, ya yi kira ga mutanen da suka yi rijista a baya amma ba su je sun karɓi katunan zaɓen su ba, da su hanzarta karɓar katunan domin amfanin kansu da ƙasar baki ɗaya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *