Juyi mulki: Sojoji sun mika wa Tinubu rahoto

[ad_1]



Rundunar Sojin Nijeriya ta miƙa wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu rahoton binciken da ta kammala kan wasu jami’an jami’anta da yunƙurin juyin mulki.

Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta miƙa rahoton ne wata biyu bayan tsare wasu hafsoshin soji 16, da ake zargi da yunƙurin juyin mulki ga Shugaba Tinubu, ciki har da wani mai muƙamin Birgediya-Janar.

Wasu manyan hafsoshin soji masu kusanci da binciken sun shaida wa wakilinmu cewa, sakamakon binciken ya samu sojojin da ake zargi da laifin yunƙurin hamɓarar da gwamnati, kamar yadda aka tuhume su.

Majiyar ta ce, duk hukuncin da Shugaban Ƙasa ya yanke kan sakamakon binciken, da shi za ɗauki mataki na gaba. Waɗanda aka dora wa alhakin gudanar da binciken sun kammala aikinsu, sun miƙa wa shugaban ƙasa rahoto.”

Da muka nemi ƙarin bayani game da abin da rahoton ya ƙunsa, majiyar ta ce, “Abin da kawai zan ce shi ne, an sami waɗanda ake zargin da laifi kuma za a hukunta su daidai da yadda doka ta tanadar, da zarar shugaban ƙasa ya ba da umarni.

“Duk da cewa ba zan iya sanin ko za a gurfanar da su a kotun soji ba, amma dai tabbas za a hukunta su daidai da dokokin aikin soji.”

‘Akwai yunƙurin juyin mulki’

Wata babbar majiya a Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar wa wakilinmu cewa rundunar tsaro ta “gabatar wa Shugaba Tinubu bayani cewa sakamakon binciken da aka kammala ya tabbatar cewa da tabbas waɗanda ake zargin su yi yunƙurin juyin mulkin, kamar yadda kafofin watsa labarai suka bayar da rahoto.”

Ta ƙara da cewa rahoton ya gano cewa mai muƙamin Birgediya-Janar ɗin da aka tsare da shi, ya samu labarin yunƙurin juyin mulkin, amma bai kai rahoto ga mahukunta ba.

“An tsare mai muƙamin Birgediya-Janar ɗin ne saboda an gano cewa ya san da batun yunƙurin amma bai kai rahoto ba,” in ji majiyar.

Sun bayyana cewa, umarnin shugaban ƙasa a kan rahoton shi ne zai zama jigon duk matakin da rundunar za ta ɗauka a kan sojojin, waɗanda a halin yanzu suke tsare a hannun Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA).

Yunƙurin wakilinmu na jin ta bakin kakakin shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga, da kuma Daniel Bwala, mashawarcin Shugaban ƙasa kan tsare-tsare, bai yi nasara ba. An kasa samun kowannensu a waya, sa’annan ba su amsa sakon WhatsApp da aka tura musu na neman ji daga gare su game da lamarin ba.

Wannan na zuwa ne kimanin wata biyu bayan wani rahoto da ya karaɗe gari ta hannun kafar labarai ta intanet, Sahara Reporters, cewa Rundunar Sojin Nijeriya ta tsare wasu hafsoshinta masu muƙamin Kyaftin zuwa Birgediya-Janar kan zargin yunƙurin kifar da gwamnati a watan Oktoban shekarar 2025.

Amma a lokacin Hedikwatar Tsaro ta Najeriya da Fadar Shugaban Ƙasa sun ƙaryata, duk da cewa labari ya karaɗe gari cewa fasa gudanar da faretin shekara-shekara na zagayowar Ranar Samun ’Yancin Najeriya na shekarar 2025, wanda aka saba gudanarwa a kowace a ranar 1 ga watan Oktoba, yana da alaƙa da zargin yunƙurin hamɓarar da gwamnati.

Daga bisani ta sanar da kama wasu hafsoshinta 16 kan abin da ta kira saɓa dokokin aiki.

Aminiya ta gano cewa a cikin sojojin da ake zargi, mutum guda ne mai muƙamin Birgediya-Janar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *