A fara duba watan Rabi’ul Auwal a ranar Asabar — Sarkin Musulmi

[ad_1]



Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duba jinjirin watan Rabi’ul Auwal 1447 daga ranar Asabar, 23 ga watan Agusta 2025.

Umarnin ya fito ne cikin wata sanarwa da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya fitar a madadin Sarkin Musulmi.

Sarkin, ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan, ya garzaya ya sanar da hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi, domin kai rahoto ga majalisar Sarkin Musulmi.

Ya kuma roƙi Allah Ya wanzar da zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.

Watan Rabi’ul Auwal na da muhimmanci a wajen Musulmai, domin a cikinsa aka haifi Manzon Allah (SAW).

A Arewacin Najeriya ana kiransa “Watan Mauludi,” saboda yawancin mutane kan yi taro da bukukuwa don tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W), tun daga farkon watan har zuwa ƙarshensa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *