NNPP Ta Caccaki Gwamna Yusuf Kan Ficewa Daga Jam’iyyar, Ta Ce “Cin Amanar Kano Da Kwankwasiyya Ne”
[ad_1]
Jam’iyyar NNPP ta bayyana matuƙar baƙin ciki kan murabus ɗin Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, daga jam’iyyar, tana mai kiran matakin a matsayin cin amana ga al’ummar Kano da kuma koma baya ga manufofin Kwankwasiyya da ya taɓa goyon baya. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Oladipo Johnson, ya fitar a ranar Juma’a.
Jam’iyyar ta ce Gwamna Yusuf ya samu nasara ne da goyon bayan tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, amma ficewarsa daga NNPP na iya mayar da jihar hannun wasu ƙungiyoyin siyasa da a cewarta sun daɗe suna adawa da ci gaban Kano da muradin jama’arta. Duk da cewa gwamnan bai bayyana inda zai koma ba, rahotanni na nuni da yiwuwar komawarsa jam’iyyar APC.
- Tinubu Da Kwankwaso Za Su Gana Yayin Da Siyasar Kano Ta Ɗauki Sabon Salo
- Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta: Kotu Ta Tsare Maƙwabta 2 Kan Bayar Da Bayanan Ƙarya A Kano
NNPP ta ƙaryata iƙirarin da gwamnan ya yi cewa jam’iyyar na fama da rikicin cikin gida da ba zai warwaru ba, tana mai cewa hakan ba shi da tushe. Ta ce jam’iyyar ta gudanar da zaɓukan shugabanci daga matakin mazaɓa har zuwa babban taron ƙasa a ranar 20 ga Disamba, 2025, a gaban hukumar INEC, tare da halartar gwamnan.
Jam’iyyar ta kuma tuna da nasarorin zaɓe da ta samu a wasu mazaɓu a Kano a watan Agusta 2025, tana mai cewa hakan ya nuna jam’iyyar na nan daram.
A ƙarshe, NNPP ta yi kira ga mambobinta da al’ummar Kano da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da zai jawo rikici. Ta jaddada cewa tarihi ya nuna masu sauya matsaya saboda son zuciya sukan fuskanci fushin jama’a, tana mai cewa amincewar al’umma ga shugabanci na gaskiya da ƙa’ida ne zai yi nasara a ƙarshe.
[ad_2]
Source link