’Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Sakkwato

[ad_1]



Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne sun kashe mutane shida a garin Baidi da ke ƙaramar hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Aminiya ta ruwaito cewa, maharan da suka kai mummunan harin a daren Larabar da ta gabata sun shiga ƙauyen ne suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya ba su damar hallaka mutane shida sannan suka tsere.

Wani jami’i a ƙaramar hukumar Tangaza ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙari domin dawo da zaman lafiya.

Wani mazaunin yankin ya alaƙanta harin rashin amincewar mutanen Baidi da Sanyinna na yi wa dokokin ’yan bindigar biyayya.

Ya ce, “wannan ba shi ne karon farko da suka kawo hari a ƙauyen nan ba. Sun saba shigowa, su kashe mutane, sannan su tsere.”

A cewarsa, ’yan bindigar sun kashe mai garin Sanyinna a wani harin da suka kai kwanakin baya, inda ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro a yankin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, tuni an yi jana’izar mutanen da aka kashe a ranar Alhamis bisa tanadin addinin Musulunci.

Hotunan jana’izar mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Al’ummar yankin na cikin baƙin ciki da fargaba sakamakon ci gaba da hare-haren ’yan bindiga, wanda ke haddasa kisa, garkuwa da mutane da kuma tilasta wa jama’a barin garuruwansu na asali.

Yankin Tangaza, wanda ya haɗa da ƙananan hukumomin Binji, Gudu da Silame, har da wasu sassan Jihar Kebbi, na fama da hare-haren ’yan bindigar Lakurawa a bayan nan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *