Gwamnan Kaduna Ya Bayyana ‘Rijana’ A Matsayin Matattarar ‘Yan Ta’adda A Nijeriya
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana yankin Rijana da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Ƙaramar Hukumar Kachia a matsayin cibiyar rashin tsaro da ayyukan ‘yan bindiga a Nijeriya.
Gwamnan ya faɗi haka ne yayin ziyarar da ya kai wa al’ummar Kurmin Wali a Ƙaramar Hukumar Kajuru, inda ake zargin ‘yan bindiga sun sace masu ibada 177 a wasu coci uku a lokacin ibada a ranar Lahadi.
- He Lifeng Ya Halarci Taron WEF Tare Da Ziyartar Kasar Switzerland
- Sin Ta Gina Tsarin Cajin Motoci Masu Amfani Da Lantarki Mafi Girma A Duniya
Ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnati na ƙoƙarin ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace.
Uba Sani ya kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soja a Kurmin Wali, ganin kusancinsa da Rijana.
Ya tunatar da cewa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya taɓa bayar da shawarar a kwashe al’ummar Rijana saboda yawaitar ayyukan ta’addanci a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar da rundunar ‘yansanda sun fara musanta labarin sace-sacen, amma daga bisani sun tabbatar da lamarin ne bayan an fitar da sunayen mutane 177 da aka sace a ranar Talata.
[ad_2]
Source link