Sakin Ƴan Bindiga 70 A Jihar Katsina: Ya Haifar Da Cece-kuce
Batun wata wasiƙar sirri da gwamnatin Jihar Katsina ta rubutawa babban jojin Jihar Katsina inda take neman a saki wasu ƴan bindiga 70 na ci gaba da ɗaukar mabanbantan ma’anoni.
Wasiƙar dai na cewa sakin ƴan bindigar na daga cikin tsarin yarjejeniyar da aka yi da ɓarayin daji lokacin zaman sulhu da aka yi da wasu al’ummomi a ƙananan hukumomin da suka dade suna fuskantar hare-haren ƴan bindiga
Abu mafi ɗaukar hankali game da wannan batu shi ne, har gobe gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa na cewa babu ruwanta da batun sulhu da ɓarayin daji.
- Gwamnatin Katsina Ta Biya Bashin Kuɗin Giratuti Na Naira Biliyan 12 — NULGE
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Zuwa yanzu dai shirye-shirye sun yi nisa na sakin manyan ƴan ta’adda a matsayin cika alƙawarin da al’umma ta ɗauka lokacin zaman sulhu da ɓarayin daji.
Bayan ɓullar wannan wasika gwamnatin Jihar Katsina ta yi ƙarin haske game da wannan takarda, wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Hon. Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya tabbatar da wannan zargi da ake yi wa gwamnatin na sakin ɓarayin daji a asirce.
Ganin cewa gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da wannan batu da ake ta cece-kuce masana harkokin tsaro suna gani wannan batu idan ya tabbatar shi ne abu mafi girman kuskure da za a yi wa harkar tsaro a Jihar Katsina.
Daga cikin abubuwan da suka fi ɗaga hankali game da kalaman kwamishinan tsaro na Jihar Katsina sun haɗa da yadda ya kaucewa tambayar da aka yi masa cewa ina tabbacin cewa za a saki ɓarayin daji a asirce?
Wannan tambaya dai bata samu amsa kyakkyawa ba, Hon. Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya bayyana cewa babu inda ba a yin musayar bursuna idan an gama yaƙi inda ya bada misali da Boko Haram da Alƙa’ida da ISIS da cewa duk an yi matsayar mutane da su.
“Ba sabon abu ne idan an yi haka, abinda ya kamata a duba shi ne irin yawan mutanen da su ƴan bindiga suka sako bayan kulla yarjejeniyar, inda yanzu ake lissafin fiye da mutum 1000 sun shaki iskar ƴanci.” Inji kwamishinan
Kazalika Hon. Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya bugi gaba da cewa a tambayi waɗanda aka yi sulhu da su da ɓarayin daji idan ba su samu zaman lafiya ba, maganar ake ɗorawa akan sikili ana yi masa hukunci da ita a yanzu.
Hon. Nasiru Mu’azu Ɗanmusa dai shi ne na gaba gaba a gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa na masu cewa babu ranar da za su yi sulhu da ƴan bindiga, amma duk ranar da ɗan bindiga ya ji wuta ya kawo kansa ya ajiye makamai to za su karbi tubansa.
Maganar kai hare-haren har gobe ba a fasa ba a ƙananan hukumomin da aka ce an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ƴan bindiga ya zama kullin sai an kai hari an sace jama’a ko dukiyoyin su ko kuma an kashe, haka abin yake kullum ranar Allah ta’ala.
A ɓangaren masana kuwa, babu wanda ya goyi bayan wannan al’amari illa ma dai suna cewa lallai ba a yi shawara da hukumomin tsoro ba kafin yanke wannan ɗanyen hukunci na sakin Ƴan bindigar.
Suna masu cewa, shi kan shi zaman sulhu wata yaudara ce da gwamnatin Jihar Katsina ta ɓullo da ita, bayan ta gama ɓaɓatun cewa babu sulhu tsakanin su da ɓarayin daji, amma abinda ya bayyana yanzu shi ne abin kunya mafi girma da wata gwamnatin a Jihar Katsina ta taɓa yi.
Mutane irin su Dakta Bashir Kurfi ba su yi mamakin wannan mataki ba saboda a cewar sa, gwamnatin ba ta al’umma take yi ba, abinda kawai ta sanya gaba shine abinda zata samu shi ya fi damunta ba halin da al’umma ke ciki ba.
Ya ƙara da cewa babu wani sulhu da aka yi illa kawai an shirya wani wasan kwaikwayo domin ayi wa al’umma rufa-rufa, amma a cewar sa inda aka ce an yi sulhu din, ɓarayin daji sun kai hari a wajen biki inda suka sa ce mutane suka raunata amarya a Katsina.
Yanzu dai wannan batu da duniya ta sanyawa ido na namen shiga halin rashin tabbas na aiwatar da abinda gwamnatin Jihar Katsina ta shirya yi ƙarƙashin ƙasa, amma abu ya tura har yanzu.
Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun jefa wasu tambayoyi akan gwamnatin Jihar Katsina musamman kwamishiniyar Shari’a, Hon. Fadila Birci inda suka ce doka ta bata ƙarfin ikon sakin ƴan bindigar amma wasu dalilai da ba a bayana ba sun hana ta yin haka.
Kwamishiniyar Shari’a dai taki cewa komi a ya yin da manema labarai suka ziyarci ofishin ta domin neman ƙarin bayani game da wannan tirka-tirka da ke wakana a Jihar Katsina
Haka kuma ana zargin cewa ana son a likawa ɓangaren kotuna laifin sakin Ƴan bindigar shi yasa aka san baban jojin Jihar Katsina ya bada umarnin a saki waɗannan ɓarayin daji.
Rahotanni sun tabbatar da cewa fiye da wata biyu aka aikewa jami’an gidan gyaran hali na Jihar Katsina da sunayen waɗanda ake san a saki da su tabbatar da wuraren da suke domin shirye-shiryen sakin su ta ƙarƙashin ƙasa.
Wani ma’aikacin gidan gyaran Hali da ya ce mu musakaya sunansa ya yi mamakin yadda wannan magana ta bulla saboda a cewar sa, ba ƙaramin kashedi aka yi masu ba game da batun, kuma tuni sun kammala aikin su, umarnin suke jira na sakin ɓarayin daji.
Yanzu dai wannan shiri na ɓoye da ya fito fili na ci gaba da nuna shakku a kan wannan gwamnati na iƙirarin da take yi na cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma na daga cikin abubuwan da ta sa gaba.
Haka kuma ta yi faduwar tasa kasa, wajen zubewar mutuncin da ake gani na ta, musamman da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ce babu shi ba sulhu da ɓarayin daji.
Sannan har gobe al’umma na tambaya ina makomar iyalan dakarun Dikko Raɗɗa fiye 100 da ƴan bindiga suka halaka yanzu kuma za a sake wasu da aka kama ana shirin yanke masu hukunci?
Sannan za a yi da makamai da ke hannun ƴan ta’adda wanda a wajen zaman sulhu ba a bayyana cewa za su ajiye makaman ba, bayan cika duk wata yarjejeniyar da aka kulla.? Wadannan tambayoyi dai na bukatar amsa, amma daga wajen gwamanti Jihar Katsina musamman Malam Dikko Umar Raɗɗa