Real Madrid ta raba gari da Xabi Alonso

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Xabi Alonso.

Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da fitaccen ɗan jaridar nan kan harkokin tamaula, Fabrizio Romano ya wallafa a shafinsa na X.

Tuni dai ƙungiyar ta maye gurbin kociyan da tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Alvaro Arbeloa.

Aminiya ta ruwaito cewa, sallamar kociyan na zuwa ne kwana guda bayan rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a wasan ƙarshe na Spanish Super Cup da Barcelona ta doke ta 3–2 a ranar Lahadi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *