Tanka ta murƙushe mutum 5 a Gombe
[ad_1]
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane biyar sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a garin Lawanti da ke Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.
Hatsarin ya faru ne a ranar Litinin, a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa da ke Lawanti, bayan da wata tanka ta ɗauko dakon iskar gas ta murƙushe wata ƙaramar mota mai ɗauke da fasinjoji.
Kwamandan FRSC na Jihar Gombe, Samson Kaura, ya shaida wa manema labarai cewa binciken farko da suka gudanar ya nuna hatsarin ya faru ne sakamakon tuƙin ganganci daga ɓangaren direban ƙaramar motar.
A cewarsa, direban ƙaramar motar da ya taso daga Gombe a hanyarsa ta zuwa Bauchi ya koma hannun tankar gas da ke shigowa Gombe, lamarin da ya janyo tsautsayin da babu makawa sai da ya auku.
“Wannan kuskure ya janyo tankar ta murƙushe ƙaramar motar, inda nan take mutane biyar suka rasa rayukansu,” in ji Kwamandan.
Ya bayyana hatsarin a matsayin abin takaici ƙwarai, yana mai kiran direbobi da su ƙara taka-tsantsan wajen kiyaye dokokin tuƙi domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Kwamandan ya ƙara da cewa sun ɗauki matakan gaggawa bayan aukuwar hatsarin, inda aka kwashe gawarwakin waɗanda suka rasu tare da tabbatar da dawowar zirga-zirgar ababen hawa yadda ya kamata a hanyar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link