AFCON 2025: Lashe Kofi Ke Gabana Ba Kyautuka Ba – Lookman

[ad_1]

Dan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ademola Lookman ya ce ba ya tunanin lashe kyautar dan wasa mafi daraja (MBP) a gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afirika da ake cigaba da bugawa a halin yanzu, ko kuma kyautar mafi yawan kwallaye a gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025, illa kawai ya mayar da hankalina wajen taimaka wa Nijeriya a kokarin da take yi na lashe gasar ta bana a Morocco.

Lookman ya kasance daya daga cikin manyan yan takarar kyaututtukan biyu bayan ya yi fice a wasanni uku da ya buga wa Super Eagles a Morocco, dan wasan mai shekaru 28 ya riga ya zura kwallaye uku kuma ya taimaka wajen zura kwallaye hudu a tawagar da Éric Chelle ke jagoranta a gasar.

Dan wasan tsakiya na Morocco Brahim Diaz wanda ya zura kwallaye hudu ne kawai ya zira kwallaye fiye da Lookman a gasar AFCON ta bana, duk da haka, dan wasan mai shekaru 28 yana da hannu a kwallayen da aka zura fiye da kowane dan wasa a gasar, zuwa yanzu Lookman ya riga ya sami matsayi a cikin mafi kyawun 11 farko a matakin rukuni na gasar.

Dan wasan gefen ya bayyana cewa babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne kungiyar ta lashe gasar, ” Ina tunani akan tawagar ne kawai, yanzu muna cikin wasan kusa da na kusa da na karshe, abokan hamayyarmu na gaba masu zafi, in ji shi bayan nasarar da Nijeriya ta samu akan Mozambikue da ci 4-0 a ranar Litinin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *