Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Sace Mutane A Taraba, Sun Ceto Mutane 3

[ad_1]

Rundunar Sojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin sace mutane tare da ceto mutane uku a Jihar Taraba.

Aikin ya gudana ne a ranar 5 ga watan Janairu, 2026, bayan sojoji sun samu bayanan sirri kan motsin wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Ƙauyen Sangai da ke Karamar Hukumar Karim Lamido.

  • AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Algeria A Wasan Kwata Fainal
  • Sojoji Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

Sojojin sun gaggauta zuwa yankin tare da bin sahun waɗanda ake zargi zuwa kan iyakar jihohin Taraba da Filato.

Da suka hangi sojojin, masu garkuwa da mutanen sun bar waɗanda suka sace tare tserewa zuwa cikin daji.

Sojojin sun ceto Nimron Umar mai shekaru 25, Abafaras Ibrahim mai shekaru 20, da Habila Yunusa mai shekaru 23.

A halin yanzu suna hannun rundunar sojin, inda ake kula da su kafin a miƙa su ga iyalansu.

Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba da ƙwarewar sojojin.

Ya jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da gudanar da ayyuka domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Taraba.

Ya kuma bukaci al’umma su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar ba su sahihan bayanai a kan lokaci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *