’Yan bindiga sun kai hari a Kebbi, sun hallaka jama’a
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Gebbe da ke cikin Ƙaramar Hukumar Shanga, Jihar Kebbi, inda suka kashe wasu daga cikin mazauna yankin.
Shaidu sun ce maharan da yawansu ya haura mutum 50 sun afka yankin ne da dare, suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙau’Yan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Gebbe da ke cikin Ƙaramar Hukumar Shanga, Jihar Kebbi, inda suka kashe wasu daga cikin mazauna yankin. tawa ba, lamarin da ya jefa jama’a cikin tsananin firgici.
Usman Magaji, wani mazaunin ƙauyen, ya bayyana yadda ya tsere tare da iyalansa: “Na gudu ta bayan gida tare da matana da ’ya’yanmu bakwai.
“’Yan bindigar suna harbi kan mai uwa da wabi. s’Sun kashe mutane, amma ba mu san adadin ba saboda kowa ya ranta a na kare.”
Wani mazaunin yankin ya ƙara tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa jama’a da dama sun rasa rayukansu, sai dai ba a iya tantance adadin waɗanda suka mutu ba saboda gudun da kowa ya yi cikin daji.
Kakakin rundunar ’yan sanda na jihar, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A cewarsa, “’Yan sanda suna aiki a kan lamarin. Jami’anmu suna nan a ƙasa domin tabbatar da tsaro.”
Ya ƙara da cewa bincike na ci gaba domin gano girman ɓarnar da aka yi, ciki har da adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata.
“Za a fitar da sanarwa a hukumance a nan gaba,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link