Ƴansanda Sun Kama Fitattun Shugabannin Ƴan Fashi Biyu A Kwara

[ad_1]

Rundunar Ƴansandan Nijeriya ta kama wasu fitattun shugabannin ƴan fashi da masu garkuwa da mutane guda biyu da ake zargi da aikata munanan laifuka a jihohin Katsina, Zamfara, da Neja da Kwara.

A cewar Kakakin Rundunar ƴansanda ta Ƙasa, CSP Benjamin Hundeyin, an kama waɗanda ake zargin ne a wani shiri na sirri da sashin Leƙen asiri na rundunar ƴansanda (FID–IRT) ya gudanar tare da hadin gwuiwar rundunar ’yansandan Jihar Kwara a ranar 19 ga Disamba, a yankin Komen–Masallaci da ke ƙaramar Hukumar Kaiama.

  • Sanata Shehu Sani Ya Buƙaci Al’ummar Kaduna Su Zaɓi Mutane Masu Mutunci A Zaɓen 2027
  • Gwamna Uba Sani Ya Tsawaita Shirin Sufurin Motocin CNG Kyauta Ga Al’ummar Jihar Kaduna

Hundeyin ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da Abubakar Usman mai laƙabin Siddi mai shekaru 26 da kuma Shehu Mohammadu mai laƙabin Jagora mai shekaru 30. An kwato babur Honda Ace 125 sabo mai darajar sama da naira miliyan 1.8, wanda aka ce kuɗin fansa ne aka saye shi da su, da kuma kuɗi Naira dubu 500 da bindiga ƙirar AK-47 tare da harsasai 20.

Binciken farko ya nuna cewa mutanen na cikin wata babbar ƙungiyar ƴan fashi da garkuwa da mutane da ke addabar al’umma a jihohi da dama, tare da zargin cewa suna kuma samar da makamai da alburusai ga sauran ƴan ta’adda. Rundunar ta ce waɗanda aka kama suna bayar da haɗin kai domin cafke sauran mambobin ƙungiyar.

Sufeto Janar na Ƴasanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yabawa jami’an bisa jajircewa da ƙwarewa, yana mai tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa rundunar za ta ci gaba da rusa ƙungiyoyin masu laifi domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bai wa ƴansanda sahihan bayanai a kan lokaci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *