Masanin Kasar Afirka Ta Kudu: Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka A Bangaren Kimiyya Da Fasaha Na Kawo Sauye-Sauye Ga Tattalin Arzikin Afirka

[ad_1]

Tashar intanet mai suna “Independent Media” ta kasar Afirka ta Kudu, ta wallafa wani bayanin da Gideon Hlamalani Chitanga ya rubuta, wanda manazarci ne a cibiyar binciken Afirka da kasar Sin a jami’ar Johannesburg ta Afirka ta Kudu, inda a cikin bayanin nasa ya ce, karkashin sabon zagayen juyin-juya-halin kimiyya da fasaha, gami da sauye-sauyen sana’o’i da ake yi cikin sauri, kasashen Afirka da kasar Sin suna kara zurfafa hadin-gwiwa a bangarorin da suka shafi fasahar sadarwa, da muhimman ababen more rayuwa ta fannin dijital, da sauran wasu sabbin fannonin kimiyya da fasaha, al’amarin da ya sanya sabon kuzari ga ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummar Afirka.

Bayanin nasa ya ce, ganin yadda sabbin fasahohin zamani ke saurin bunkasa, ciki har da nazarin manyan alkaluma wato “big data”, da fasahar AI wato kirkirarriyar basira, kasashen Afirka na da damar amfani da su, gami da ingantacciyar alakar hadin-gwiwa ta fannin kimiyya da fasaha, don kawo sauye-sauye ga salon tattalin arziki. An kuma yi hasashen cewa, zuwa shekara ta 2030, wadannan fasahohin za su bayar da gudummawar karuwar tattalin arzikin Afirka, wadda yawanta ya kai dala kimanin tiriliyan 1.5.

Kazalika, hadin-gwiwar Afirka da Sin na taka muhimmiyar rawa ga rage gibin fasahar dijital da kasashen Afirka ke fuskanta. A nan gaba kuma, ya dace bangarorin biyu su ci gaba da habaka hadin-gwiwa a bangaren kimiyya da fasaha, da mayar da shi daya daga cikin muhimman fannonin taimakawa kasashen Afirka, kawo sauye-sauye masu dorewa ga tattalin arziki, da zaman rayuwar al’umma gami da samun zamanantarwa. (Murtala Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *