Ba za mu lamunci karin kuɗin mota na zalunci ba —FCCPC

[ad_1]



Hukumar Kare Gasa da Masu Amfani da Kaya ta Ƙasa (FCCPC) ta gargaɗi direbobi da kamfanonin sufuri cewa za ta hukunta duk wani karin kuɗi na zalunci ko rashin adalci.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Daraktan Huldar Kamfanoni na hukumar, Ondaje Ijagwu, a ranar Lahadi, sakamakon ƙorafe-ƙorafen da ake ta yi kan yadda direbobi ke ta ƙara kuɗin mota ba bisa ƙa’ida ba a fadin ƙasar.

Ya bayyana cewa karin kuɗin mota a lokacin bukukuwan Kirsimeti ba laifi ba ne, tare da FCCPC ta amince cewa yawan buƙata a lokacin bukukuwa, matsalolin aiki da wasu sahihan dalilai na iya shafar farashin kuɗin mota a irin wannan lokaci.

Sai dai ta jaddada cewa masu amfani da motoci suna da haƙƙin samun bayani mai inganci, gaskiya da kuma a kan lokaci kan kuɗin mota kafin su fara tafiya.

“Duk wani ƙarin kuɗi dole ne a bayyana shi a fili kuma a yi amfani da shi cikin adalci,” in ji hukumar.

Hukumar ta ƙara da cewa ƙorafe-ƙorafen na fitowa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin rage farashin man fetur a wasu sassan ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *