Tinubu ya gana da shugabannin ƙwadago kan zanga-zangar rashin tsaro




Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin ƙwadago a ranar Talata kan zanga-zangar ƙasa da su neka shirya, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kauce wa tsunduma yajin aiki.

Taron ya gudana ne da tsakar dare a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da kuma gwamnonin APC suka halarta, ƙarƙashin jagorancin shugabansu kuma Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma.

Da yake magana da ’yan jarida bayan taron, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce taron na neman shawara ne, kuma ƙungiyar ƙwadago za ta tattauna a cikin gida kafin ta yanke hukunci na ƙarshe.

“Mun zo neman shawara da Shugaban Ƙasa kuma mun gama. Dole ne mu koma taronmu mu ci gaba gobe. Zuwa gobe za mu fitar da sakamako,” in ji Ajaero.

Da aka tambaye shi ko zanga-zangar za ta ci gaba kamar yadda aka tsara, shugaban NLC ya ce ba a yanke hukunci ba tukuna, yana mai jaddada cewa ƙungiyar ƙwadago tana aiki ne a haɗe.

“Ko zan yi zanga-zangar ko ba za a yi ba, zan sanar da ku. Ba ƙungiya ce da mutum ɗaya ke tafiyarwa. Za mu koma mu nazarci duk abin da Shugaban Ƙasa ya faɗa mana sannan mu ci gaba daga nan,” in ji shi.

A nasa bangaren, Gwamna Uzodimma ya bayyana taron a matsayin wani ɓangare na tattaunawa da ake ci gaba da yi tsakanin manyan masu ruwa da tsaki, yana mai cewa tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa.

“Tattaunawa ta ci gaba. Mun yi muhawara kuma a ƙarshe za ku san abin da ya kamata ku sani,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne maslahar ƙasa.

“Abin da ’yan Najeriya ya kamata su sani shi ne duk masu ruwa da tsaki suna aiki ne don ƙasar. ’Yan kwadago, gwamnati da talakawa duk suna aiki ne wajen bauta wa ƙasa,” in ji Uzodimma.

Haka kuma, Kakakin Shugaban Kasa Bayo Onanuga, ya tabbatar da taron a wani rubutu da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce Tinubu ya gana da shugabannin NLC tare da Uzodimma; Gwamnan Edo, Monday Okpebholo; Gwamnan Kebbi, Dr Nasir Idris; da Karamin Ministan Ƙwadago, Mrs Nkeiruka Onyejeocha.

“Shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya jagoranci shugabannin ƙwadago zuwa taron da aka gudanar da yammacin Talata a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja,” in ji shi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *