Kotun ta ɗaure wani mutum shekara 5 kan yunƙurin fyaɗe
[ad_1]
Wata Babbar Kotun Jihar Kebbi ta yanke wa Ibrahim Isah, daga Ƙaramar Hukumar Zuru, hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari kan yunƙurin fyade ga wata yarinya ’yar shekara 10.
Da take yanke hukunci, Mai Shari’a Maryam Abubakar Kaoje ta ce an same shi da laifin yunƙurin aikata fyade, laifi da doka ta tanadi hukunci a ƙarƙashin Sashe na 58 na Dokar Penal Code ta Jihar Kebbi, 2021.
Tun da farko, an gurfanar da Isah ne da tuhume-tuhume biyu na fyaɗe da kuma aikata mummunan alfasha, ƙarƙashin Sashe na 259 da 261 na Penal Code.
Sai dai kotun ta ce shaidu da aka gabatar ba su tabbatar da cikakken laifin fyaɗe ba.
Bisa bayanan da ke cikin kundin kotu, ɓangaren tuhuma ƙarƙashin jagorancin Daraktan Gurfanar da Laifuka (DPP), Lawal Hudu Garba, SAN, ya gabatar da shaidu biyar tare da gabatar da hujjoji uku, ciki har da bayanan amincewar laifi na wanda ake tuhuma da aka rubuta da Turanci da Hausa, da kuma rahoton likita na yarinyar da abin ya shafa.
Ɓangaren kariya kuwa, ƙarƙashin jagorancin Lauya S.M. DanYaro, ya gabatar da shaida guda ɗaya baya ga wanda ake tuhuma.
A hukuncinta, Mai Shari’a Kaoje ta ce bayanan da ke cikin takardar amincewar laifi sun tabbatar da cewa an yi yunƙurin aikata fyaɗe, wanda laifi ne da ya fi sauƙi fiye da wanda aka fara tuhumar sa da shi.
Saboda haka, ta same shi da laifi a ƙarƙashin Sashe na 58 na Penal Code.
Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari, tare da tarar Naira 50,000. Idan ya kasa biyan tarar, zai ƙara shafe shekara daya a gidan yari.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link