Za A Wallafa Makalar Xi Dangane Da Matakan Kwaskwarima Ga JKS

[ad_1]


A gobe Litinin ne za a wallafa makalar shugaban kwamitin kolin JKS Xi Jinping, dangane da aiwatar da matakan yiwa JKS kwaskwarima. Makalar za ta fito ne cikin wallafa ta 23, ta muhimmiyar mujallar Qiushi ta kwamitin kolin JKS.

Makalar ta ce karfafa cikakke, kuma managarcin tsarin jagorancin jam’iyya ta hanyar farawa da kyautata da’a, muhimmiyar kwarewa ce da jam’iyyar ta samu, wadda za ta taimaka mata wajen cimma nasarar yiwa kai kwaskwarima a sabon zamani.

Bugu da kari, makalar ta ce za a aiki tukuru wajen cimma nasarar zamanantarwa, yayin da jam’iyyar take fuskantar yanayi mai sarkakiya na jagoranci. Kyautata fahimtar matakin yiwa jam’iyyar kwaskwarima yana da muhimmiyar ma’awa, wanda kuma zai daukaka kima, da amincewar jama’a ga jam’iyyar, tare da karfafa gwiwar membobi da jami’ai na jam’iyyar, da tabbatar da managarcin goyon bayan siyasa, domin samar da ci gaba mai matukar inganci.

A daya bangaren, makalar ta ce ya zama wajibi membobi da jami’an jam’iyyar su sanya a ransu cewa, har kullum al’umma ne ke samar da dukkanin iko, kuma wajibi ne a yi amfani da shi ta hanyar da ta dace. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *