Manoman Rake Sun Tabka Asarar Kimanin Naira Biliyan Biyu A Kano

[ad_1]


Manoma da dama a Jihar Kano, sun bayyana fargabarsu, kan barkewar annobar wata cuta da ta yi sanadiyyar lalata Raken da suka shuka a gonakinsu.

Wannan annoba, ta bulla ne a kananan hukumomi uku da ake noman Raken a fadin jihar, wadda kuma ta lalata hektoci da dama da hakan zai iya haifar da karancinsa a bana.

Wasu daga cikin manoman Raken da abin ya shafa, sun bayyana cewa; sun gano bullar cutar ne a daidai lokacin da suka fara shirye-shiyen girbin Raken. A cewarsu, asarar da annobar ta jawo, ta kai ta akalla Naira biliyan biyu, inda kuma suka sanar da cewa; zai yi musu wuya, su sake yin wani noman a kakar noma ta badi, matukar mahukunta ba su dauki matakan gaggawa kan lamarin ba. Sun bayyana cewa, cutar ta yi wa daukacin gonakin da aka shuka Raken matukar illa, musamman a yankunan Dan Hassan, Garin Kaya, Tofa da kuma Gamadan.

A cewar daya daga cikin manoman Raken a garin Kura, Malam Kawu Hayi, “Ba mu tsammaci cutar ta lalata gonakin Raken kamar haka ba, inda ya ce; lamarin ya fi yin kamari a garin Gamadan, wanda nan ne babban yankin da aka fi yin nomansa da kuma hada-hadar kasuwancinsa.Akasari dai, noman Raken shi ne kusan sana’ar da al’ummar yankin suka fi mayar da hankali a kai, wajen samun kudaden shiga, inda bullar cutar a yanzu za ta iya jawo samun marasa aikin yi”.

Rahotanni sun bayyana cewa, Raken da ba a riga an girbe shi ba, ya yi bakikkirin wasu kuma sun bushe. Shi ma wani nanomin Raken da ke yankin, Malam Isah Shu’aibu ya bayyana cewa; yankin ne kan gaba wajen noman Rake a daukacin fadin Arewacin kasar.”Muna kan shirye-shiryen girbe Raken, cutar ta bulla, wadda kuma ta lalata akasarin gonakin manoman Raken baki-daya, kazalika mun zuba dimbin kudade a aikin gonakin tare da bata lokacinmu, wajen yin aiki a gonakin namu, amma yanzu, komai ya lalace,” a cewarsa.

Har ila yau, ya yi gargadi da cewa; idan har ba a yi gaggawar dakile yaduwar cutar ba, hakan zai iya sanya wa manoma da dama a yankunan yin watsi da noman Rake a shekara mai zuwa, inda kuma wasunsu.

Bisa wani bincike da aka gudanar, an gano cewa; illar cutar ta fara haifar da hauhawar farashinsa da kuma karancinsa. Wani babban dilan Raken, Danbaba Yunusa Dan Hassan, ya sanar da cewa; nan ba da jimawa ba, Raken zai yi karanci a wasu kasuwannin, matukar ba a dauki matakan gaggawa kan dakile yaduwar cutar ba, domin lamarin ya fi karfin manomansa, wajen lalubo mafita a kan matsalar.

Kazalika, manoman sun bayyana cewa; akwai bukatar mahukunta a bangaren aikin noma, su tura malaman gona domin duba irin illar da cutar ta yi a gonakin tare kuma da bayar da shawara kan lamarin.

Wani malamin gona a garin Kura Salisu Sa’ad, ya tabbatar da bullar cutar wanda ya ce; tuni ya tura zuwa gonakin da iftila’in ya afku, domin tantance irin barnar da cutar ta yi don daukar matakan da suka dace.Wata mai gudanar da bincike a Hukumar Aikin Noma (IITA), Dakta Wajiha Abdullahi Mu’az, ta danganta annobar a matsayin wata babbar barazana da ke bukatar daukar matakan gaggawa, domin dakile yaduwarta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *