PRP Ta Gargadi Sabon Shugaban PDP Kan Neman Taimakon Kasashen Waje A Rikicin Jam’iyya
[ad_1]
Jam’iyyar PRP ta gargadi sabon shugaban PDP na kasa, Tanimu Turaki (SAN), da ya janye kalamusa na kiran Shugaban Amurka, Donald Trump, don tsoma baki a rikicin jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da shugaban PRP na kasa, Falalu Bello, ya fitar, ya bayyana kiran a matsayin rashin hankali da hadari kuma wanda bai dace da kasar ba.
A yayin da yake magana da ‘yan jarida bayan samun shiga cikin hedikwatar jam’iyyar PDP a Abuja bayan dogon rikici tsakanin magoya bayan bangarorin adawa a ranar Talata, Turaki ya roki Shugaba Trump da ya tsoma baki a rikicin jam’iyyar.
“Ina so in yi kira ga Shugaba Trump, abin da ke faruwa a yanzu ba kawai kisan kare dangi ba ne ga kiristocin Nijeriya har da ma dimokuradiyyar,” in ji Turaki.
Amma a martaninta, PRP ta ce irin wannan kalamai na matukar ruguza kasa tare da ci gaba da kawo rudani idan har shugabannin siyasa na furta irin wannan kalamai masu daci.
Ta ce, “Wannan kalamai yana nuna wata matsala ta rashin amincewa da dorewar Nijeriya da ciiyoyin dimokuradiyya, ba tare da la’akari da yadda mutane suke kallonsu ba, da kuma karfin hadin kan mutanen kasar.
“Hakan cin zarafi ne ga ‘yancin kai, ‘yancin mallaka, da darajar Nijeriya tare da wulakanta dabi’u da dimbin ‘yan kasa masu kishin Nijeriya.
“Nijeriya kasa ce mai ‘yanci kuma an kafa ta a matsayin jamhuriya tare da iyakokin da aka ayyana, tana da gwamnati mai ‘yanci tare da tsoma bakin kowacce kasar waje ba.
“Muna kira ga Tanimu Turaki da PDP da su janye wannan furuci mai zafi da rashin fahimta nan take. Haka kuma, muna kira ga dukkan shugabannin Nijeriya da su kiyaye darajar kasarmu kuma su kaurace wa duk wani lamari da zai iya rage ikonmu ta hanyar neman taimako daga kasashen waje. Karfin Nijeriya yana cikin mutanenta, hukumominta, da kuma jajircewarta mara yankewa wajen gina kasa mai adalci da hadin kai.
“Dole ne a warware matsalolinmu ta hanyar tattaunawa ta cikin gida, hanyoyin dimokradiyya masu karfi, da jagoranci mai kishin kasa, ba ta hanyar karfi daga kasashen waje ba. Bai kamata a nemi taimakon kasashen waje ba a harkokin cikin gida don amfanin kashin kai,” in ji jam’iyyar.
[ad_2]
Source link