Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya

[ad_1]



An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya.

Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar.

Thompson mai shekaru 43, ta karɓi lambar yabon ne daga masu shirya gasar nunin ƙarfi ta duniya, kwanaki biyu bayan kammala bikin a Arlington da ke birnin Texas na Amurka, wanda aka gudanar a daga 20 zuwa 23 ga watan Nuwamba.

Gasar nuna ƙarfin ta duniya tana da tsauraran ƙa’idoji, inda ake bai wa ’yan takara damar fafatawa ne kawai bisa jinsinsu na asali domin tabbatar da adalci.

A gasar bana, Thompson ta ƙare a matsayi na biyu bayan kammala fannonin wasanni guda shida da suka haɗa da ɗaga nauyi da sauran gwaje-gwaje a rukunin mata.

Lokacin da aka ayyana Jammy Booker a matsayin zakara gabanin a gano namiji ne ya sauya jinsi


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *