Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Kare Nasarar Yakin Duniya Na II
[ad_1]
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da Raja Dato’ Nushirwan bin Zainal Abidin, darakta janar na majalisar tsaron Malaysia, inda ya yi kira ga kasashen biyu su kare nasarar yakin duniya na II, kuma kada su bari wani ya mayar da hannun agogo baya.
Raja Dato’ Nushirwan bin Zainal Abidin, na ziyara a kasar Sin ne domin halartar taron tattaunawa na Sin da Malaysia karo na 2 kan tafiyar da harkokin da suka shafi teku.
A cewar Wang Yi, ya kamata a hada kai sosai wajen yaki da ra’ayin bangare guda da na kariyar cinikayya, da kuma daukaka tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa da bayar da gudunmuwa ga daidaituwar tattalin arzikin duniya. (FMM)
[ad_2]
Source link