Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka manta da su a Gombe
Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar UNICEF da gwamnatin Jihar Gombe, sun shirya taron wayar da kai da ’yan jarida domin yaƙi da cututtukan da ba a cika kula da su ba.
Ofishin UNICEF na Bauchi ya haɗa kai da ’yan jarida da JPHCDA da wakiliyar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Hauwa Abubakar, domin tattaunawa kan yadda za a rage yaɗuwar cututtukan a jihar.
A taron, ’yan jarida sun samu damar jin bayanai daga masana da kuma yadda aikace-aikacen yaƙi da cututtukan ke tasiri a cikin al’umma.
Gwamnatin Jihar Gombe tana ware Naira miliyan 25 duk shekara domin yaƙi da NTDs, amma har yanzu akwai wuraren da ake buƙatar ƙarin tallafi.
Ƙungiyar Amen Health Care and Empowerment Foundation, ta ce tun 2015 ake samun ci gaba wajen yaƙi da cututtuka kamar onchocerciasis, lymphatic filariasis, da schistosomiasis.
Ƙungiyar ta kuma ce an yi wa waɗanda ke fama cututtukan tiyata kyauta.
Wakilin UNICEF, Hillary Adie, ya ce matsanancin talauci da rashin tsafta na taimaka wa yaɗuwar cututtukan.
Ya jaddada muhimmancin tsaftar muhallin zama.
Hauwa Abubakar, ta yi kira da a ƙara haɗa kai tsakanin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Ita kuwa Shugabar UNICEF ta Bauchi, Dokta Nuzhat Rafique, ta yaba wa Gombe kan ci gaban da ta samu, tare da roƙon ’yan jarida su ci gaba da wayar da kan jama’a game da cututtukan.