EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo.
Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo mai ɗauke da hoton tsohon gwamnan da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin.
Hukumar ta ce tana neman Mista Sylva ne bisa zargin wata badaƙalar kuɗi da yawansu ya kai dala miliyan 14.8.
EFCC ta ce tana zargin tsohon gwamnan da karkatar da kuɗin da aka yi niyyar amfani da su wajen gina matatar man fetur a ƙasar.
Hukumar ta ce wata kotu ce a Jihar Legas ta bayar da sammacin kama tsohon ƙaramin ministan na man fetur na Najeriya.
EFCC ta kuma buƙaci duk wanda yake da bayanan da za su taimaka wajen kama tsohon gwamnan ya gabatar mata da su.