Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta



Rundunar Sojin Nijeriya, Runduna ta 6, ta ce jami’anta sun kama wasu da ake zargi da satar mai su 14 tare da kwace sama da lita 20,000 a yankin Neja Delta.

Haka kuma, rundunar ta ce sojoji sun tarwatsa haramtattun matatun mai 14 ba bisa ka’ida ba a lokacin wani samame na musamman a wuraren da ake kyautata tsammanin badaƙalar muggan ayyuka a wuraren.

Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojan Runduna ta 6, Jonah Danjuma, ya fitar a Fatakwal a safiyar Litinin.

An cimma wannan nasara ne a wani samame da aka kai tsawon makonni biyu a wasu wuraren da ake zargin ana aikata laifuka a yankin mai arzikin mai, in ji sanarwar.

Rundunar Sojin ta yi alƙawarin ƙara ƙaimi kan tarwatsa duk wata haramtacciyar matata a yankin Neja Delta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *