An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai




Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 ​​a cikin  masai.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a.

Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai.

“Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Daraktan, Sani Anas ta samu kiran gaggawa daga Usman Adamu da misalin ƙarfe 9:27 na safiyar ranar Alhamis, 6 ga watan Nuwamba, 2025, inda ya bayar da rahoton ibtila’in da wata mata ta faɗa cikin ramin masai a ƙauyen Sarai da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu,” a cikin sanarwar.

“Jami’anmu na sashen agajin gaggawa daga hedikwatar hukumar ta isa wurin, inda ta gano wata mata mai suna Habiba Ado mai shekara 96, wanda ’yan uwanta suka ce tana fama da taɓin hankali,” in ji shi.

Abdullahi ya bayyana cewa, ‘yan uwanta ​​sun shafe kwanaki huɗu suna nemanta kafin a gano gawarta a cikin masai ranar Alhamis.

“Sun kuma yi kira ga mai gidan da ya rufe ramin masan don hana afkuwar irin haka nan gaba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jami’an ceto sun gano  matar daga cikin ramin, amma an tabbatar da mutuwar ta.

Tuni dai aka miƙa gawarta ga Hakimin Unguwa, Alhaji Musa Muhammad domin yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *