Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa
[ad_1]
Wata kotu a Ƙasar Jamus ta yanke wa wani ma’aikacin jinya hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin kashe marasa lafiya 10 da kuma yunƙurin kashe ƙarin wasu 27 ta hanyar yi musu allurar guba.
Kotun da ke birnin Aachen a yammacin Jamus, ta tabbatar da cewa mutumin mai shekaru 44 ya aikata laifukan ne tsakanin watan Disamban 2023 zuwa Mayun 2024 a asibitin Wuerselen.
Kotun ta bayyana cewa laifin da ya aikata babban laifi ne, wanda zai hana shi samun ’yanci bayan shekaru 15 kamar yadda ake yadda a irin waɗannan shari’o’in.
Ba a bayyana sunan mutumin ba, amma masu gabatar da ƙara sun ce yana “wasa da rayuwar marasa lafiyar” da yake kula da su.
Lauyansa ya roƙi kotu ta wanke shi lokacin da aka fara shari’ar a watan Maris.
Masu gabatar da ƙara sun ce mutumin yana yi wa marasa lafiya, waɗanda mafi yawansu tsofaffi ne, allurar magunguna masu sa barci da rage zafi don rage wahalar aikinsa a lokacin dare.
Sun kuma bayyana cewa mutumin yana da matsalar halayya, ba ya nuna tausayawa ga marasa lafiya, kuma bai nuna nadama ba a lokacin shari’ar.
Haka kuma, sun ce yana amfani da morphine da midazolam, wani magani da ake amfani da shi a wasu lokuta wajen aiwatar da hukuncin kisa a Amurka.
An kuma sake zarginsa da yin aiki ba tare da bin ƙa’ida ba, da kuma rashin nuna ƙwazo a aikinsa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link