Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya
[ad_1]
Wani ɗan majalisar dokokin Amurka mai suna Riley Moore, ya zargi tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da hannu a kisan Kiristoci a Nijeriya.
Moore, ya yi wannan zargi ne bayan Kwankwaso ya soki maganganun da Amurka ta yi na shirin ɗaukar matakin soji a kan Nijeriya.
A rubutun da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Moore ya ce, “Gwamna, kana da hannu a kashe Kiristoci. Kai ne ka ƙaddamar da Shari’ar Musulunci kuma ka sanya hukuncin kisa ga wanda ake zargi da yi wa addini ɓatanci.”
Kwankwaso, wanda ya jagoranci Kano lokacin da aka kafa ƙaddamar da Shari’ae Musulunci a shekarar 2000, ya yi martani game da kalaman Shugaba Donald Trump na Amurka game da matsalar tsaro a Nijeriya.
Ya gargaɗi Amurka da kada ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Nijeriya, inda ya bayyana cewa matsalar tsaro a ƙasar ba ta da bambance tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Ya roƙi Amurka ta taimaka ta hanyar fasaha da diflomasiyya, maimakon barazanar yaƙi, tare da kira ga ‘yan ƙasar da su haɗa kansu.
A gefe guda, Riley Moore ya bayyana cewa zai nemi a gudanar da bincike kan abin da ya kira “yi wa Kiristoci kisan kiyashi” a Nijeriya, yayin da Trump ya nuna yiwuwar ɗaukar matakin soja.
Sai dai gwamnatin Nijeriya ta ƙaryata zargin kisan kiyashin, ta bayyana cewa ƙasar tana kare haƙƙin dukkanin ’yan ƙasa ba tare da la’akari da addininsu ba.
Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai ’yancin addini, kuma gwamnatinsa na ci gaba da aiki tare da shugabannin addinai domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar.
[ad_2]
Source link